* Bawan Allah shi ne duk wani mai wa'azi yana kira zuwa ga Allah. Bã ya halatta a gare shi ya bar waɗanda yake yi wa wa'azi su kai fagen bauta Masa shi kansa. Sai ya gaya musu gaskiyar matsayinsa, kamar yadda Allah Ya faɗa wa AnnabinSa, kuma Ya umarce shi da ya gaya wa waɗanda yake yi wa wa'azi.
* ldan Allah Yã aiko wani manzonsa da wani umurni ko hani zuwa ga mutãne to zai sanya mala'iku gaba gare shi da bãya gare shi suna gãdin sa dõmin kada wani Shaiɗãni ya kusance shi har ya sanya shi mantuwa ko kuskure, har ya iyar da manzancin nan kamar yadda yake.