Traduzione dei Significati del Sacro Corano - Traduzione hausa - Abubakar Gomi

Numero di pagina:close

external-link copy
14 : 72

وَأَنَّا مِنَّا ٱلۡمُسۡلِمُونَ وَمِنَّا ٱلۡقَٰسِطُونَۖ فَمَنۡ أَسۡلَمَ فَأُوْلَٰٓئِكَ تَحَرَّوۡاْ رَشَدٗا

"Kuma lalle ne mũ akwai a cikinmu, waɗanda suka mĩƙa wuya, kuma akwai a cikinmu karkatattu. to, wanda ya mĩƙa wuya waɗancan kam sun nufi shiryuwa." info
التفاسير:

external-link copy
15 : 72

وَأَمَّا ٱلۡقَٰسِطُونَ فَكَانُواْ لِجَهَنَّمَ حَطَبٗا

"Kuma amma karkatattu sai suka kasance makãmashi ga Jahannama." info
التفاسير:

external-link copy
16 : 72

وَأَلَّوِ ٱسۡتَقَٰمُواْ عَلَى ٱلطَّرِيقَةِ لَأَسۡقَيۡنَٰهُم مَّآءً غَدَقٗا

"Kuma dã sun tsayu* sõsai a kan hanya, dã lalle Mun shãyar da su ruwa mai yawa." info

* Tsayuwa sosai wato su bautawa Allah kamar yadda Allah Ya umarce su, su yi Masa ɗa'a saboda Yã wadãta su.

التفاسير:

external-link copy
17 : 72

لِّنَفۡتِنَهُمۡ فِيهِۚ وَمَن يُعۡرِضۡ عَن ذِكۡرِ رَبِّهِۦ يَسۡلُكۡهُ عَذَابٗا صَعَدٗا

"Domin Mu jarraba su a ciki, kuma wanda ya kau da kai daga tuna Ubangijinsa, Ubangijinsa zai shigar da shi azãba mai hauhawa." info
التفاسير:

external-link copy
18 : 72

وَأَنَّ ٱلۡمَسَٰجِدَ لِلَّهِ فَلَا تَدۡعُواْ مَعَ ٱللَّهِ أَحَدٗا

"Kuma lalle ne wurãren sujada na Allah ne, saboda haka kada ku kira kõwa tãre da Allah (da su, a cikinsu)." info
التفاسير:

external-link copy
19 : 72

وَأَنَّهُۥ لَمَّا قَامَ عَبۡدُ ٱللَّهِ يَدۡعُوهُ كَادُواْ يَكُونُونَ عَلَيۡهِ لِبَدٗا

"Kuma, lalle ne shi, a lõkacin da bãwan Allah* ke kiran Sa sun yi kusa su zama kamar shirgi a kansa." info

* Bawan Allah shi ne duk wani mai wa'azi yana kira zuwa ga Allah. Bã ya halatta a gare shi ya bar waɗanda yake yi wa wa'azi su kai fagen bauta Masa shi kansa. Sai ya gaya musu gaskiyar matsayinsa, kamar yadda Allah Ya faɗa wa AnnabinSa, kuma Ya umarce shi da ya gaya wa waɗanda yake yi wa wa'azi.

التفاسير:

external-link copy
20 : 72

قُلۡ إِنَّمَآ أَدۡعُواْ رَبِّي وَلَآ أُشۡرِكُ بِهِۦٓ أَحَدٗا

Ka ce: "lna kiran Ubangijina ne kawai, kuma bã zan tãra kowa da Shi ba." info
التفاسير:

external-link copy
21 : 72

قُلۡ إِنِّي لَآ أَمۡلِكُ لَكُمۡ ضَرّٗا وَلَا رَشَدٗا

Ka ce: "Lalle ne, nĩ bã ni mallakar wata cũta gare ku, kuma bã ni mallakar wani alhẽri." info
التفاسير:

external-link copy
22 : 72

قُلۡ إِنِّي لَن يُجِيرَنِي مِنَ ٱللَّهِ أَحَدٞ وَلَنۡ أَجِدَ مِن دُونِهِۦ مُلۡتَحَدًا

Ka ce: "Lalle ne, nĩ kõwa bã ya iya cẽtona daga Allah, kuma bã zan iya sãmun mafaka ba daga gare Shi." info
التفاسير:

external-link copy
23 : 72

إِلَّا بَلَٰغٗا مِّنَ ٱللَّهِ وَرِسَٰلَٰتِهِۦۚ وَمَن يَعۡصِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَإِنَّ لَهُۥ نَارَ جَهَنَّمَ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدًا

"Fãce iyarwa, daga Allah, da manzancinsa. To, wanda ya sãɓa wa Allah da Manzon Sa, to, lalle yana da wutar Jahannama suna mãsu dawwama a cikinta, har abada." info
التفاسير:

external-link copy
24 : 72

حَتَّىٰٓ إِذَا رَأَوۡاْ مَا يُوعَدُونَ فَسَيَعۡلَمُونَ مَنۡ أَضۡعَفُ نَاصِرٗا وَأَقَلُّ عَدَدٗا

Har idan sun ga abin da ake yi musu gargaɗi da shi, to, zã su san wanda ya zama mafi raunin mataimaki da mafi ƙarancin adadi. info
التفاسير:

external-link copy
25 : 72

قُلۡ إِنۡ أَدۡرِيٓ أَقَرِيبٞ مَّا تُوعَدُونَ أَمۡ يَجۡعَلُ لَهُۥ رَبِّيٓ أَمَدًا

Ka ce: "Ban sani ba a kusa ne abin da ake yi muku gargaɗi da shi, ko Ubangijina Ya sanya masa dõgon ajali!" info
التفاسير:

external-link copy
26 : 72

عَٰلِمُ ٱلۡغَيۡبِ فَلَا يُظۡهِرُ عَلَىٰ غَيۡبِهِۦٓ أَحَدًا

"Shi ɗai ne Masanin fake sabõda haka, bã Ya bayyana gaibinsa ga kowa." info
التفاسير:

external-link copy
27 : 72

إِلَّا مَنِ ٱرۡتَضَىٰ مِن رَّسُولٖ فَإِنَّهُۥ يَسۡلُكُ مِنۢ بَيۡنِ يَدَيۡهِ وَمِنۡ خَلۡفِهِۦ رَصَدٗا

"Fãce ga wanda Yã yarda da shi, wato wani manzo sa'an nan lalle ne, zai sanya* gãdi a gaba gare shi da bãya gare shi." info

* ldan Allah Yã aiko wani manzonsa da wani umurni ko hani zuwa ga mutãne to zai sanya mala'iku gaba gare shi da bãya gare shi suna gãdin sa dõmin kada wani Shaiɗãni ya kusance shi har ya sanya shi mantuwa ko kuskure, har ya iyar da manzancin nan kamar yadda yake.

التفاسير:

external-link copy
28 : 72

لِّيَعۡلَمَ أَن قَدۡ أَبۡلَغُواْ رِسَٰلَٰتِ رَبِّهِمۡ وَأَحَاطَ بِمَا لَدَيۡهِمۡ وَأَحۡصَىٰ كُلَّ شَيۡءٍ عَدَدَۢا

"Dõmin Ya san lalle, sun iyar da sãƙonnin Ubangijinsu, kuma (Shi Ubangijin) Yã kẽwaye su da sani, kuma Yã lissafe dukan kõme da ƙididdiga." info
التفاسير: