Traduzione dei Significati del Sacro Corano - Traduzione hausa - Abubakar Gomi

Numero di pagina:close

external-link copy
52 : 42

وَكَذَٰلِكَ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ رُوحٗا مِّنۡ أَمۡرِنَاۚ مَا كُنتَ تَدۡرِي مَا ٱلۡكِتَٰبُ وَلَا ٱلۡإِيمَٰنُ وَلَٰكِن جَعَلۡنَٰهُ نُورٗا نَّهۡدِي بِهِۦ مَن نَّشَآءُ مِنۡ عِبَادِنَاۚ وَإِنَّكَ لَتَهۡدِيٓ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Kuma kamar wancan Mun aika wani rũhi (rai mai haɗa jama'a) zuwa gare ka, daga gare Mu. Ba ka kasance kã san abin da yake littãfi ba, kõ abin da Yake ĩmãni, kuma amma Mun sanya shi (rũhin, watau Alƙur'ãni) wani haske ne, Munã shiryar da wanda Muke so daga cikin bãyĩn Mu game da shi. Kuma Lalle kai, haƙĩƙa, kanã shiryarwa zuwa ga hanya, madaidaiciya. info
التفاسير:

external-link copy
53 : 42

صِرَٰطِ ٱللَّهِ ٱلَّذِي لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ أَلَآ إِلَى ٱللَّهِ تَصِيرُ ٱلۡأُمُورُ

Hanyar Allah wanda ke da mulkin abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa. To, zuwa ga Allah kawai al'amura ke kõmãwa. info
التفاسير: