Traduzione dei Significati del Sacro Corano - Traduzione hausa - Abubakar Gomi

Numero di pagina:close

external-link copy
16 : 42

وَٱلَّذِينَ يُحَآجُّونَ فِي ٱللَّهِ مِنۢ بَعۡدِ مَا ٱسۡتُجِيبَ لَهُۥ حُجَّتُهُمۡ دَاحِضَةٌ عِندَ رَبِّهِمۡ وَعَلَيۡهِمۡ غَضَبٞ وَلَهُمۡ عَذَابٞ شَدِيدٌ

Kuma waɗannan da ke jãyayya a cikin al'amarin Allah daga bãyan an karɓa masa, hujjarsu ɓãtãcciya ce a wurin Ubangijinsu, kuma akwai fushi a kansu, kuma sunã da wata azãba mai tsanani. info
التفاسير:

external-link copy
17 : 42

ٱللَّهُ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ وَٱلۡمِيزَانَۗ وَمَا يُدۡرِيكَ لَعَلَّ ٱلسَّاعَةَ قَرِيبٞ

Allah ne Wanda Ya saukar da Littãfi da gaskiya, da sikeli. Kuma me ya sanar da kai (cẽwa anã) tsammãnin Sa'ar kusa take? info
التفاسير:

external-link copy
18 : 42

يَسۡتَعۡجِلُ بِهَا ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِهَاۖ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مُشۡفِقُونَ مِنۡهَا وَيَعۡلَمُونَ أَنَّهَا ٱلۡحَقُّۗ أَلَآ إِنَّ ٱلَّذِينَ يُمَارُونَ فِي ٱلسَّاعَةِ لَفِي ضَلَٰلِۭ بَعِيدٍ

Waɗanda ba su yi ĩmãni da ita ba, (sũ) ke nẽman gaggautõwarta. Alhãli kuwa waɗanda suka yi ĩmãni, mãsu tsõro ne daga gare ta, kuma sun sani, cẽwa ita gaskiya ce. To, lalle ne waɗanda ke shakka a cikin Sa'a, haƙĩƙa, sunã a cikin ɓata Mai nĩsa. info
التفاسير:

external-link copy
19 : 42

ٱللَّهُ لَطِيفُۢ بِعِبَادِهِۦ يَرۡزُقُ مَن يَشَآءُۖ وَهُوَ ٱلۡقَوِيُّ ٱلۡعَزِيزُ

Allah Mai tausasãwa ne ga bãyinsa. Yanã azurta wanda yake so, alhãli kuma Shĩ ne Maiƙarfi, Mabuwãyi. info
التفاسير:

external-link copy
20 : 42

مَن كَانَ يُرِيدُ حَرۡثَ ٱلۡأٓخِرَةِ نَزِدۡ لَهُۥ فِي حَرۡثِهِۦۖ وَمَن كَانَ يُرِيدُ حَرۡثَ ٱلدُّنۡيَا نُؤۡتِهِۦ مِنۡهَا وَمَا لَهُۥ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِن نَّصِيبٍ

Wanda ya kasance yanã nufin nõman Lãhira zã Mu ƙãra masa a cikin nõmansa, kuma wanda ya kasance yanã nufin nõman dũniya, zã Mu sam masa daga gare ta, alhãli kuwa bã shi da wani rabo a cikin Lãhira. info
التفاسير:

external-link copy
21 : 42

أَمۡ لَهُمۡ شُرَكَٰٓؤُاْ شَرَعُواْ لَهُم مِّنَ ٱلدِّينِ مَا لَمۡ يَأۡذَنۢ بِهِ ٱللَّهُۚ وَلَوۡلَا كَلِمَةُ ٱلۡفَصۡلِ لَقُضِيَ بَيۡنَهُمۡۗ وَإِنَّ ٱلظَّٰلِمِينَ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Kõ sunã da waɗansu abõkan tãrayya (da Allah) waɗanda suka shar'anta musu, game da addini, abin da Allah bai yi izni ba da shi? Kuma bã dõmin kalmar hukunci ba, da lalle, an yi hukunci a tsakãninsu. Kuma lalle azzãlumai sunã da azãba mai raɗaɗi. info
التفاسير:

external-link copy
22 : 42

تَرَى ٱلظَّٰلِمِينَ مُشۡفِقِينَ مِمَّا كَسَبُواْ وَهُوَ وَاقِعُۢ بِهِمۡۗ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ فِي رَوۡضَاتِ ٱلۡجَنَّاتِۖ لَهُم مَّا يَشَآءُونَ عِندَ رَبِّهِمۡۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡفَضۡلُ ٱلۡكَبِيرُ

Kanã ganin azzãlumai sunã mãsu tsõro daga abin da suka sanã'anta alhãli kuwa shi abin tsoron, mai aukuwa ne gare su, kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai sunã a cikin fadamun Aljanna sunã da abin da suke so a wurin Ubangijinsu. Waccan fa ita ce falala mai girma. info
التفاسير: