* Ɓõye lõkacin Ƙiyãma a bãyan bayãnin tabbatar aukuwarta yanã daga cikin ni'imõmin Allah, dõmin mai hankali ya yi tattãli sabõda ita.
* Tsuntsãye hõrarru a cikin sararin sama, ana nufi da su, a ganĩna, Allah ne Ya san haƙĩƙa, su ne jirãgen sama, sabõda ambaton hõrewa tãre da sũ a cikin sararin samãniya, dõmin abin da aka hõre, ana hõronsa ne dõmin a ci amfãninsa a lõkaci da wurin hõron. Tsuntsãyen al'ãda bã su da wani amfãni a gare mu a lõkacin da suke a cikin sãrãrin sama. Sabõda haka bãbu wani abu, sai jirgin sama. Bã zã a ce anã nufin shãho ba a lõkacin farauta, dõmin wannan amfãni yã yi kaɗan bisa ga abin da sũrar take ƙidãyãwa na ni'imõmin Allah a kan mutãne gabã ɗaya. Farauta keɓãɓɓiya ce ga mutãnen ƙauye kawai.