Traduzione dei Significati del Sacro Corano - Traduzione hausa - Abubakar Gomi

external-link copy
79 : 16

أَلَمۡ يَرَوۡاْ إِلَى ٱلطَّيۡرِ مُسَخَّرَٰتٖ فِي جَوِّ ٱلسَّمَآءِ مَا يُمۡسِكُهُنَّ إِلَّا ٱللَّهُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ

Shin ba su ga tsuntsãye* ba sunã hõrarru cikin sararin sama bãbu abin da yake riƙe su fãce Allah? Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni. info

* Tsuntsãye hõrarru a cikin sararin sama, ana nufi da su, a ganĩna, Allah ne Ya san haƙĩƙa, su ne jirãgen sama, sabõda ambaton hõrewa tãre da sũ a cikin sararin samãniya, dõmin abin da aka hõre, ana hõronsa ne dõmin a ci amfãninsa a lõkaci da wurin hõron. Tsuntsãyen al'ãda bã su da wani amfãni a gare mu a lõkacin da suke a cikin sãrãrin sama. Sabõda haka bãbu wani abu, sai jirgin sama. Bã zã a ce anã nufin shãho ba a lõkacin farauta, dõmin wannan amfãni yã yi kaɗan bisa ga abin da sũrar take ƙidãyãwa na ni'imõmin Allah a kan mutãne gabã ɗaya. Farauta keɓãɓɓiya ce ga mutãnen ƙauye kawai.

التفاسير: