Fassarar Ma'anonin Alqura'ni - Fassarar Hausa - Abubakar Gumi

Lambar shafi:close

external-link copy
48 : 74

فَمَا تَنفَعُهُمۡ شَفَٰعَةُ ٱلشَّٰفِعِينَ

Sabõda haka cẽton mãsu cẽto bã zai amfãne su ba. info
التفاسير:

external-link copy
49 : 74

فَمَا لَهُمۡ عَنِ ٱلتَّذۡكِرَةِ مُعۡرِضِينَ

Haba! Me ya same su, suka zama mãsu bijirewa daga wa'azin gaskiya. info
التفاسير:

external-link copy
50 : 74

كَأَنَّهُمۡ حُمُرٞ مُّسۡتَنفِرَةٞ

Kamar dai sũ, jãkuna firgitattu ne. info
التفاسير:

external-link copy
51 : 74

فَرَّتۡ مِن قَسۡوَرَةِۭ

Sun gudu daga zãki. info
التفاسير:

external-link copy
52 : 74

بَلۡ يُرِيدُ كُلُّ ٱمۡرِيٕٖ مِّنۡهُمۡ أَن يُؤۡتَىٰ صُحُفٗا مُّنَشَّرَةٗ

A'aha! Kõwãne mutum daga cikinsu yanã son a zo masa da takardu (da sũnansa) ana wãtsãwa info
التفاسير:

external-link copy
53 : 74

كَلَّاۖ بَل لَّا يَخَافُونَ ٱلۡأٓخِرَةَ

A'aha! Kai dai, bã su jin tsõron Lãhira. info
التفاسير:

external-link copy
54 : 74

كَلَّآ إِنَّهُۥ تَذۡكِرَةٞ

A'aha! Lalle ne, shi (Alƙur'ãni) tunãtarwa ce. info
التفاسير:

external-link copy
55 : 74

فَمَن شَآءَ ذَكَرَهُۥ

Dõmin wanda ya so, ya tuna. info
التفاسير:

external-link copy
56 : 74

وَمَا يَذۡكُرُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُۚ هُوَ أَهۡلُ ٱلتَّقۡوَىٰ وَأَهۡلُ ٱلۡمَغۡفِرَةِ

Kuma bã zã su tuna ba fãce idan Allah Ya so, Shi ne Ya cancanta a bi Shi da taƙawa kuma Ya cancanta ga Ya yi gãfara. info
التفاسير: