Fassarar Ma'anonin Alqura'ni - Fassarar Hausa - Abubakar Gumi

external-link copy
19 : 5

يَٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ قَدۡ جَآءَكُمۡ رَسُولُنَا يُبَيِّنُ لَكُمۡ عَلَىٰ فَتۡرَةٖ مِّنَ ٱلرُّسُلِ أَن تَقُولُواْ مَا جَآءَنَا مِنۢ بَشِيرٖ وَلَا نَذِيرٖۖ فَقَدۡ جَآءَكُم بَشِيرٞ وَنَذِيرٞۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Yã Mutãnen Littãfi! Lalle Manzon Mu yã je muku yanã bayyana muku, a kan lõkacin fatara daga manzanni, dõmin kada ku ce: "wani mai bayar da bushãra bai zo mana ba, kuma haka wani mai gargaɗi bai zo ba." To, haƙĩƙa, mai bãyar da bushãra da mai gargaɗi sunje muku. Kuma Allah ne, a kan dukkan kõme, Mai ĩkon yi. info
التفاسير: