Fassarar Ma'anonin Alqura'ni - Fassarar Hausa - Abubakar Gumi

external-link copy
203 : 2

۞ وَٱذۡكُرُواْ ٱللَّهَ فِيٓ أَيَّامٖ مَّعۡدُودَٰتٖۚ فَمَن تَعَجَّلَ فِي يَوۡمَيۡنِ فَلَآ إِثۡمَ عَلَيۡهِ وَمَن تَأَخَّرَ فَلَآ إِثۡمَ عَلَيۡهِۖ لِمَنِ ٱتَّقَىٰۗ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّكُمۡ إِلَيۡهِ تُحۡشَرُونَ

Kuma ku ambaci Allah a cikin kwanuka ƙidayayyu.* To, wanda ya yi gaggawa a cikin kwana biyu, to, bãbu laifi a kansa, kuma wanda ya jinkirta, to, bãbu laifi a kansa, ga wanda ya yi taƙawa. Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma ku sani cewa lalle ne kũ, zuwa gare Shi ake tãrã ku. info

* Bayãnin kabbarõri, bãyan sallõlin farillai gõma sha biyar, anã fãrawa da sallar azahar ta ranar salla a ƙãre da sallar asuba ta rãna ta huɗu daga rãnar salla. Kwãnukan Mina uku ne daga rãnar salla, sai ga wanda ya yi gaggawa ya fita daga Mina bãyan fitar rãnar nan kuma gabãnin fãɗuwar rãna.

التفاسير: