* Bãyan da ya faɗi cewa Allah Yanã kira, kiran gaskiya a cikin ãyã ta l4, kuma waɗansu mutãne sun ƙi karɓar kiran Allah, sai sunã kiran waɗansu abũbuwa dabam, sai ya bayyana, a nan, sakamakon wanda ya karɓi kiran Allah sãmun ruwan sha, sabõda Mai abu ne Ya kirãwo shi, Ya kuma bã shi, ya sha a hankali kwance, sa'an nan kuma Allah zai bã shi abin da ya fi ruwan kyau, watau Aljanna. Amma wanda ya ƙi karɓãwa, to, yã yi hasãra biyu, bai sãmi ruwan da ya yi kiran wani ya bã shi ba, sa'an nan kuma ya haɗu da azãbar da take zai iya bãyar da dukan abin da ya mallaka dõmin ya yi fansar kansa da ita.