Traduction des sens du Noble Coran - La traduction en haoussa - Abou Bakr Jomy

Al'rahman

external-link copy
1 : 55

ٱلرَّحۡمَٰنُ

(Allah) Mai rahama. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 55

عَلَّمَ ٱلۡقُرۡءَانَ

Yã sanar da Alƙur'ani. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 55

خَلَقَ ٱلۡإِنسَٰنَ

Yã halitta mutum. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 55

عَلَّمَهُ ٱلۡبَيَانَ

Yã sanar da shi bayãni (magana). info
التفاسير:

external-link copy
5 : 55

ٱلشَّمۡسُ وَٱلۡقَمَرُ بِحُسۡبَانٖ

Rãnã da watã a kan lissãfi suke. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 55

وَٱلنَّجۡمُ وَٱلشَّجَرُ يَسۡجُدَانِ

Kuma tsirrai mãsu yãɗo da itãce sunã tawãlu'i. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 55

وَٱلسَّمَآءَ رَفَعَهَا وَوَضَعَ ٱلۡمِيزَانَ

Kuma samã Ya ɗaukaka ta, Kuma Yã aza sikẽli. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 55

أَلَّا تَطۡغَوۡاْ فِي ٱلۡمِيزَانِ

Dõmin kada ku karkatar da sikẽlin. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 55

وَأَقِيمُواْ ٱلۡوَزۡنَ بِٱلۡقِسۡطِ وَلَا تُخۡسِرُواْ ٱلۡمِيزَانَ

Kuma ku daidaita awo da ãdalci, kuma kada ku rage sikẽlin. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 55

وَٱلۡأَرۡضَ وَضَعَهَا لِلۡأَنَامِ

Kuma ƙasã Yã aza ta dõmin tãlikai. info
التفاسير:

external-link copy
11 : 55

فِيهَا فَٰكِهَةٞ وَٱلنَّخۡلُ ذَاتُ ٱلۡأَكۡمَامِ

A cikinta akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno mai kwasfa. info
التفاسير:

external-link copy
12 : 55

وَٱلۡحَبُّ ذُو ٱلۡعَصۡفِ وَٱلرَّيۡحَانُ

Da ƙwãya mai sõshiya da ƙamshi. info
التفاسير:

external-link copy
13 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangjinku *kuke ƙaryatãwa? info

* Asalin lamiri "ku" yanã nũni ne ga nau'i biyu, watau mutãne da aljannu, sai dai bãbu lamirin abu biyu kawai a cikin Hausa, sai na jama'a. Jam'i a luggar Hausa ya fara daga biyu.

التفاسير:

external-link copy
14 : 55

خَلَقَ ٱلۡإِنسَٰنَ مِن صَلۡصَٰلٖ كَٱلۡفَخَّارِ

Yã halitta mutum daga ƙẽkasasshen yumɓu kumar kasko. info
التفاسير:

external-link copy
15 : 55

وَخَلَقَ ٱلۡجَآنَّ مِن مَّارِجٖ مِّن نَّارٖ

Kuma ya halitta aljani daga bira daga wutã. info
التفاسير:

external-link copy
16 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
17 : 55

رَبُّ ٱلۡمَشۡرِقَيۡنِ وَرَبُّ ٱلۡمَغۡرِبَيۡنِ

Ubangjin mafita biyu na rãnã, kuma Ubangijin mafãɗã biyu na rãnã. info
التفاسير:

external-link copy
18 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
19 : 55

مَرَجَ ٱلۡبَحۡرَيۡنِ يَلۡتَقِيَانِ

Yã garwaya tẽku biyu (ruwan dãɗi da na zartsi) sunã haɗuwa. info
التفاسير:

external-link copy
20 : 55

بَيۡنَهُمَا بَرۡزَخٞ لَّا يَبۡغِيَانِ

A tsakãninsu akwai shãmaki, bã za su ƙetare haddi ba. info
التفاسير:

external-link copy
21 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
22 : 55

يَخۡرُجُ مِنۡهُمَا ٱللُّؤۡلُؤُ وَٱلۡمَرۡجَانُ

Lu'ulu'u da murjãni na fita daga gare su. info
التفاسير:

external-link copy
23 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
24 : 55

وَلَهُ ٱلۡجَوَارِ ٱلۡمُنشَـَٔاتُ فِي ٱلۡبَحۡرِ كَٱلۡأَعۡلَٰمِ

Kuma Yanã da manyan jirãge, waɗanda ake ƙãgãwa a cikin tẽku kamar manyan duwãtsu. info
التفاسير:

external-link copy
25 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
26 : 55

كُلُّ مَنۡ عَلَيۡهَا فَانٖ

Dukkan wanda ke kanta* mai ƙãrẽwa ne. info

* Yanã nufin ƙasa.

التفاسير:

external-link copy
27 : 55

وَيَبۡقَىٰ وَجۡهُ رَبِّكَ ذُو ٱلۡجَلَٰلِ وَٱلۡإِكۡرَامِ

Kuma Fuskarar Ubangijinka, Mai girman Jalala da karimci, ita ce take wanzuwa. info
التفاسير:

external-link copy
28 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
29 : 55

يَسۡـَٔلُهُۥ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ كُلَّ يَوۡمٍ هُوَ فِي شَأۡنٖ

wanda ke a cikin sammai da ƙasã yanã rõƙon Sa (Allah), a kullum Allah na a cikin wani sha'ani. info
التفاسير:

external-link copy
30 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
31 : 55

سَنَفۡرُغُ لَكُمۡ أَيُّهَ ٱلثَّقَلَانِ

Zã mu ɗauki lõkaci sabõda ku, yã kũ *mãsu nauyin halitta biyu! info

* Mutãne da aljannu.

التفاسير:

external-link copy
32 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
33 : 55

يَٰمَعۡشَرَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِ إِنِ ٱسۡتَطَعۡتُمۡ أَن تَنفُذُواْ مِنۡ أَقۡطَارِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ فَٱنفُذُواْۚ لَا تَنفُذُونَ إِلَّا بِسُلۡطَٰنٖ

Ya jama'ar aljannu da mutãne! Idan kunã iya zarcẽwa daga sãsannin sammai da ƙasã to ku zarce. Bã za ku iya zarcẽwaba fãce da wani dalĩli. info
التفاسير:

external-link copy
34 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
35 : 55

يُرۡسَلُ عَلَيۡكُمَا شُوَاظٞ مِّن نَّارٖ وَنُحَاسٞ فَلَا تَنتَصِرَانِ

Anã sako wani harshe daga wata wutã a kanku, da narkakkiyar tagulla. To, bã zã ku nẽmi taimako ba? info
التفاسير:

external-link copy
36 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
37 : 55

فَإِذَا ٱنشَقَّتِ ٱلسَّمَآءُ فَكَانَتۡ وَرۡدَةٗ كَٱلدِّهَانِ

Sa'an nan idan sama ta tsãge kuma ta zama jã kamar jar fãta. info
التفاسير:

external-link copy
38 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
39 : 55

فَيَوۡمَئِذٖ لَّا يُسۡـَٔلُ عَن ذَنۢبِهِۦٓ إِنسٞ وَلَا جَآنّٞ

To, a ran nan bã zã a tambayi wani mutum laifinsa ba, kuma haka aljani. info
التفاسير:

external-link copy
40 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
41 : 55

يُعۡرَفُ ٱلۡمُجۡرِمُونَ بِسِيمَٰهُمۡ فَيُؤۡخَذُ بِٱلنَّوَٰصِي وَٱلۡأَقۡدَامِ

zã a iya sanin mãsu laifi da alãmarsu, sabõda haka sai a kãma kwarkaɗarsu da sãwãyensu. info
التفاسير:

external-link copy
42 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
43 : 55

هَٰذِهِۦ جَهَنَّمُ ٱلَّتِي يُكَذِّبُ بِهَا ٱلۡمُجۡرِمُونَ

Wannan Jahannama ce wadda mãsu laifi ke ƙaryatãwa game da ita. info
التفاسير:

external-link copy
44 : 55

يَطُوفُونَ بَيۡنَهَا وَبَيۡنَ حَمِيمٍ ءَانٖ

Sunã kẽwaya a tsakaninta da ruwan ɗimi mai tsananin tafasa. info
التفاسير:

external-link copy
45 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
46 : 55

وَلِمَنۡ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِۦ جَنَّتَانِ

Kuma wanda ya ji tsõron tsayãwa a gaba ga Ubangijinsa yanã da Aljanna biyu. info
التفاسير:

external-link copy
47 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
48 : 55

ذَوَاتَآ أَفۡنَانٖ

Mãsu rassan itãce. info
التفاسير:

external-link copy
49 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
50 : 55

فِيهِمَا عَيۡنَانِ تَجۡرِيَانِ

A cikinsu akwai marẽmari biyu sunã gudãna. info
التفاسير:

external-link copy
51 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
52 : 55

فِيهِمَا مِن كُلِّ فَٰكِهَةٖ زَوۡجَانِ

A cikinsu akwai nau'i biyu daga kõwane 'ya'yan itãcen marmari. info
التفاسير:

external-link copy
53 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
54 : 55

مُتَّكِـِٔينَ عَلَىٰ فُرُشِۭ بَطَآئِنُهَا مِنۡ إِسۡتَبۡرَقٖۚ وَجَنَى ٱلۡجَنَّتَيۡنِ دَانٖ

Sunã gincire a kan waɗansu shimfiɗu cikinsu tufãfin alharĩni mai kauri ne kuma nũnannun 'yã'yan itãcen Aljannar biyu kusakusa suke. info
التفاسير:

external-link copy
55 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
56 : 55

فِيهِنَّ قَٰصِرَٰتُ ٱلطَّرۡفِ لَمۡ يَطۡمِثۡهُنَّ إِنسٞ قَبۡلَهُمۡ وَلَا جَآنّٞ

A cikinsu akwai mãtã mãsu taƙaita ganinsu, wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗebe budurcinsu ba kuma haka wani aljani. info
التفاسير:

external-link copy
57 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
58 : 55

كَأَنَّهُنَّ ٱلۡيَاقُوتُ وَٱلۡمَرۡجَانُ

Kamar dai su yaƙũtu ne da murjãni. info
التفاسير:

external-link copy
59 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
60 : 55

هَلۡ جَزَآءُ ٱلۡإِحۡسَٰنِ إِلَّا ٱلۡإِحۡسَٰنُ

Shin, kyautatãwa nã da wani sakamako? (Ã'aha) fãce kyautatãwa. info
التفاسير:

external-link copy
61 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
62 : 55

وَمِن دُونِهِمَا جَنَّتَانِ

Kuma baicinsu akwai waɗansu gidãjen Aljanna biyu. info
التفاسير:

external-link copy
63 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
64 : 55

مُدۡهَآمَّتَانِ

Mãsu duhun inuwa. info
التفاسير:

external-link copy
65 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
66 : 55

فِيهِمَا عَيۡنَانِ نَضَّاخَتَانِ

A cikinsu akwai marẽmari biyu masu kwarãrar ruwa. info
التفاسير:

external-link copy
67 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
68 : 55

فِيهِمَا فَٰكِهَةٞ وَنَخۡلٞ وَرُمَّانٞ

A cikinsu akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno darummãni. info
التفاسير:

external-link copy
69 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
70 : 55

فِيهِنَّ خَيۡرَٰتٌ حِسَانٞ

A cikinsu, akwai wasu mãtã mãsu kyawun hãlãye, mãsu kyaun halitta. info
التفاسير:

external-link copy
71 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
72 : 55

حُورٞ مَّقۡصُورَٰتٞ فِي ٱلۡخِيَامِ

Mãsu farin idãnu da baƙinsu waɗanda aka tsare a cikin haimõmi. info
التفاسير:

external-link copy
73 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
74 : 55

لَمۡ يَطۡمِثۡهُنَّ إِنسٞ قَبۡلَهُمۡ وَلَا جَآنّٞ

Wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗẽbe budurcinsu ba, kuma haka wani aljani. info
التفاسير:

external-link copy
75 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
76 : 55

مُتَّكِـِٔينَ عَلَىٰ رَفۡرَفٍ خُضۡرٖ وَعَبۡقَرِيٍّ حِسَانٖ

Sunã gincire a kan wasu matãsai mãsu kõren launi da katĩfun Abkara kyãwãwa. info
التفاسير:

external-link copy
77 : 55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
78 : 55

تَبَٰرَكَ ٱسۡمُ رَبِّكَ ذِي ٱلۡجَلَٰلِ وَٱلۡإِكۡرَامِ

Sũnan Ubangjinka, Mai girman Jalãla da Karimci, ya tsarkaka. info
التفاسير: