* Yã fãra Sũrar da tambayar Sahabbai ga Annabi cewa. wãne ne ya fi cancanta da dũkiyar ganĩmar da aka sãmu a yãƙin Badar Babba, samãri mayãƙa kõ tsõfaffi mãsu bãyar da shãwara da ra'ayõyinsu, mãsu kyau. Sa'annan ya yi jawãbi da cewa: "Ka ce ganimar ta Allah ce da ManzonSa," sabõda dalĩlan da suke tafe ga ayõyin da suke biye. Ana nufi wanke sõja daga jãyayya a kan dũkiya. AllahYa fi sani.
* Asalin fitar Musulmi zuwa Badar shi ne Annabi ya ji lãbãrin Abu Sufyãna yã fito daga Makka da ãyari zuwa Shãm, watau "Syria" , sai ya fita dõmin a kãma shi, suka sãmi Abu Sufyãna yã shige da dũkiya, sabõda haka Annabi daga Badar ya kõma Madĩna. Wannan fita, anã kiran ta Badar karama. Da Abu Sufyãna ya sãmi lãbãri, sai ya aika wa Kuraishãwa, dõmin su fito, su tsare dũkiyarsu daga Musulmi. Annabi, da ya ji lãbãrin kõmõwar Abu Sufyãna, sai ya fita tãre da jama'arsa, wanda ya ji Yanã son fita, kuma yanã da abin hawa. Abu Sufyãna tãre da ãyari sũ ne wajen da bãbu ƙaya. Yaƙin Kuraishãwa shĩ ne wajen da yake da ƙaya. Musulmi a tsakiya. Abu Sufyãna ya saki hanya ya tsĩra .Ya nemi Kuraishãwa da su kõma, Abu Jahal ya ce sai Allah Yã yi hukunci a tsakãninsu da Muhammadu wanda ya kãtse zumuntã, ya bar addinin iyãye.