《古兰经》译解 - 豪萨语翻译 - 艾布·拜克尔·朱米。

Al'anfal

external-link copy
1 : 8

يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡأَنفَالِۖ قُلِ ٱلۡأَنفَالُ لِلَّهِ وَٱلرَّسُولِۖ فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَصۡلِحُواْ ذَاتَ بَيۡنِكُمۡۖ وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

Suna tambayar ka* ga ganĩma. ka ce: "Ganĩma ta Allah daManzonSa ce. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku gyãra abin da yake a tsakãninku, kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, idan kun kasance Mũminai." info

* Yã fãra Sũrar da tambayar Sahabbai ga Annabi cewa. wãne ne ya fi cancanta da dũkiyar ganĩmar da aka sãmu a yãƙin Badar Babba, samãri mayãƙa kõ tsõfaffi mãsu bãyar da shãwara da ra'ayõyinsu, mãsu kyau. Sa'annan ya yi jawãbi da cewa: "Ka ce ganimar ta Allah ce da ManzonSa," sabõda dalĩlan da suke tafe ga ayõyin da suke biye. Ana nufi wanke sõja daga jãyayya a kan dũkiya. AllahYa fi sani.

التفاسير:

external-link copy
2 : 8

إِنَّمَا ٱلۡمُؤۡمِنُونَ ٱلَّذِينَ إِذَا ذُكِرَ ٱللَّهُ وَجِلَتۡ قُلُوبُهُمۡ وَإِذَا تُلِيَتۡ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُهُۥ زَادَتۡهُمۡ إِيمَٰنٗا وَعَلَىٰ رَبِّهِمۡ يَتَوَكَّلُونَ

Abin sani kawai, nũminai sũ ne waɗanda suke idan an ambaci, Allah, zukãtansu su firgita, kuma idan an karanta ãyõyinSa a kansu, su ƙãrã musu wani ĩmãni, kuma ga Ubangijinsu suke dõgara. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 8

ٱلَّذِينَ يُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَمِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ يُنفِقُونَ

Waɗanda suke tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azũrtã su sunã ciyarwa.* info

* Watau sunã yin ibãda ta jiki da ta dũkiya wãjiba da nãfila.

التفاسير:

external-link copy
4 : 8

أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ حَقّٗاۚ لَّهُمۡ دَرَجَٰتٌ عِندَ رَبِّهِمۡ وَمَغۡفِرَةٞ وَرِزۡقٞ كَرِيمٞ

Waɗannan sũ ne mũminai da gaskiya. Sunã da darajõji a wurin Ubangijinsu, da wata gãfara da arziki na karimci. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 8

كَمَآ أَخۡرَجَكَ رَبُّكَ مِنۢ بَيۡتِكَ بِٱلۡحَقِّ وَإِنَّ فَرِيقٗا مِّنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ لَكَٰرِهُونَ

Kamar yadda Ubangijinka Ya fitar da kai daga gidanka da gaskiya, alhãli kuwa lalle wani ɓangare na mũminai, haƙĩƙa, sunã ƙyãma. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 8

يُجَٰدِلُونَكَ فِي ٱلۡحَقِّ بَعۡدَ مَا تَبَيَّنَ كَأَنَّمَا يُسَاقُونَ إِلَى ٱلۡمَوۡتِ وَهُمۡ يَنظُرُونَ

Sunã jãyayya da kai a cikin (sha'anin) gaskiya a bãyan tã bayYanã, kamar dai lalle anã kõra su zuwa ga mutuwa ne alhãli kuwa sunã kallo. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 8

وَإِذۡ يَعِدُكُمُ ٱللَّهُ إِحۡدَى ٱلطَّآئِفَتَيۡنِ أَنَّهَا لَكُمۡ وَتَوَدُّونَ أَنَّ غَيۡرَ ذَاتِ ٱلشَّوۡكَةِ تَكُونُ لَكُمۡ وَيُرِيدُ ٱللَّهُ أَن يُحِقَّ ٱلۡحَقَّ بِكَلِمَٰتِهِۦ وَيَقۡطَعَ دَابِرَ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Kuma a lõkacin* da Allah Yake yi muku alkawari da ɗayan ƙungiya biyu, cẽwa lalle ita tãku ce: kuma kunã gũrin cẽwa lalle ƙungiya wadda bã ta da ƙaya ta kasance gare ku, kuma Allah Yanã nufin Ya tabbatar da gaskiya da kalmõminSa, kuma Ya kãtse ƙarshen kãfirai; info

* Asalin fitar Musulmi zuwa Badar shi ne Annabi ya ji lãbãrin Abu Sufyãna yã fito daga Makka da ãyari zuwa Shãm, watau "Syria" , sai ya fita dõmin a kãma shi, suka sãmi Abu Sufyãna yã shige da dũkiya, sabõda haka Annabi daga Badar ya kõma Madĩna. Wannan fita, anã kiran ta Badar karama. Da Abu Sufyãna ya sãmi lãbãri, sai ya aika wa Kuraishãwa, dõmin su fito, su tsare dũkiyarsu daga Musulmi. Annabi, da ya ji lãbãrin kõmõwar Abu Sufyãna, sai ya fita tãre da jama'arsa, wanda ya ji Yanã son fita, kuma yanã da abin hawa. Abu Sufyãna tãre da ãyari sũ ne wajen da bãbu ƙaya. Yaƙin Kuraishãwa shĩ ne wajen da yake da ƙaya. Musulmi a tsakiya. Abu Sufyãna ya saki hanya ya tsĩra .Ya nemi Kuraishãwa da su kõma, Abu Jahal ya ce sai Allah Yã yi hukunci a tsakãninsu da Muhammadu wanda ya kãtse zumuntã, ya bar addinin iyãye.

التفاسير:

external-link copy
8 : 8

لِيُحِقَّ ٱلۡحَقَّ وَيُبۡطِلَ ٱلۡبَٰطِلَ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡمُجۡرِمُونَ

Dõmin Ya tabbatar da gaskiya, kuma Ya ɓãta ƙarya, kuma kõdã mãsu laifi sun ƙi. info
التفاسير: