Übersetzung der Bedeutungen von dem heiligen Quran - Die Übersetzung in Hausa - Abu Bakr Jomy.

Nummer der Seite:close

external-link copy
49 : 34

قُلۡ جَآءَ ٱلۡحَقُّ وَمَا يُبۡدِئُ ٱلۡبَٰطِلُ وَمَا يُعِيدُ

Ka ce: "Gaskiya ta zo, kuma ƙarya bã ta iya fara (kome) kuma bã ta iya mayarwa." info
التفاسير:

external-link copy
50 : 34

قُلۡ إِن ضَلَلۡتُ فَإِنَّمَآ أَضِلُّ عَلَىٰ نَفۡسِيۖ وَإِنِ ٱهۡتَدَيۡتُ فَبِمَا يُوحِيٓ إِلَيَّ رَبِّيٓۚ إِنَّهُۥ سَمِيعٞ قَرِيبٞ

Ka ce: "Idan na ɓace, to, inã ɓacẽwa ne kawai a kan kaina. Kuma idan na shiryu, to, sabõda abin da Ubangijina Yake yõwar wahayi ne zuwa a gare ni. Lalle Shĩ Mai ji ne, Makusanci." info
التفاسير:

external-link copy
51 : 34

وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذۡ فَزِعُواْ فَلَا فَوۡتَ وَأُخِذُواْ مِن مَّكَانٖ قَرِيبٖ

Kuma dã kã gani, a lõkacin da suka firgita, to, bãbu kuɓuta, kuma aka kãma su daga wuri makusanci. info
التفاسير:

external-link copy
52 : 34

وَقَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِهِۦ وَأَنَّىٰ لَهُمُ ٱلتَّنَاوُشُ مِن مَّكَانِۭ بَعِيدٖ

Kuma suka ce: "Mun yi ĩmãni da Shi." To inã zã su sãmu kãmãwa daga wuri mai nisa? info
التفاسير:

external-link copy
53 : 34

وَقَدۡ كَفَرُواْ بِهِۦ مِن قَبۡلُۖ وَيَقۡذِفُونَ بِٱلۡغَيۡبِ مِن مَّكَانِۭ بَعِيدٖ

Kuma lalle sun kãfirta da Shi a gabãnin haka, kuma sunã jĩfa da jãhilci daga wuri mai nĩsa. info
التفاسير:

external-link copy
54 : 34

وَحِيلَ بَيۡنَهُمۡ وَبَيۡنَ مَا يَشۡتَهُونَ كَمَا فُعِلَ بِأَشۡيَاعِهِم مِّن قَبۡلُۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ فِي شَكّٖ مُّرِيبِۭ

Kuma an shãmakance a tsakãninsu da tsakãnin abin da suke marmari, kamar yadda aka aikata da irin ƙungiyõyinsu a gabãninsu. Lalle sũ sun kasance a cikin shakka mai sanya kõkanto. info
التفاسير: