* Ƙissar Dãwũda da ta Sulaimãn sunã nũna yadda Allah ke sauƙaƙe wa bãyinsa hanyar ibãda da ta sãmun abinci da sauƙi idan sun mayar da al'amuransu gare shi. Ƙissar sabaãwa tanã nũna yadda Allah ke karɓe wadãta daga wanda ya kãfirce Masa
* Allah na saka wa kãfirai gwargwadon aikinsu, kuma Yanã yin falala ga mũmini da kyautar da ta fi aikinsa.
* Tafiya a tsakãnin Yemen, ƙasar Saba'awa da Syria, watau Sham, ƙasã mai albarka, ƙasarAnnabãwa kuma ƙasa mai yawan ruwa da itãce.
* Muka sanya saba'ãwa suka wãtse a cikin waɗansu ƙasãshe sabõda ruwa ya halaka ƙasãrsu, sa'an nan kuma ta bũshe bãbu wadãta, har ana cewa 'Sun yi rarrabar Saba'ãwa' watau sun wãtse.