Qurani Kərimin mənaca tərcüməsi - Hövsa dilinə tərcümə - Əbu Bəkir Cumi.

external-link copy
47 : 8

وَلَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ خَرَجُواْ مِن دِيَٰرِهِم بَطَرٗا وَرِئَآءَ ٱلنَّاسِ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِۚ وَٱللَّهُ بِمَا يَعۡمَلُونَ مُحِيطٞ

Kada ku kasance kamar waɗanda suka fita daga gidãjensu,* sunã mãsu alfahari da yin riya ga mutãne, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah. Kuma Allah ne ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa. info

* Kada Musulmi su fita zuwa yãƙi da nũna alfahari da kiɗe-kiɗe da giya da mãtã da maganganun alfãsha, kamar yadda Kuraishãwa suka fita zuwa Badar; ku fita da tawãlu'i da zikirin Allah.

التفاسير: