Qurani Kərimin mənaca tərcüməsi - Hövsa dilinə tərcümə - Əbu Bəkir Cumi.

Səhifənin rəqəmi:close

external-link copy
40 : 34

وَيَوۡمَ يَحۡشُرُهُمۡ جَمِيعٗا ثُمَّ يَقُولُ لِلۡمَلَٰٓئِكَةِ أَهَٰٓؤُلَآءِ إِيَّاكُمۡ كَانُواْ يَعۡبُدُونَ

Kuma rãnar da Allah Ya ke tãra su gabã ɗaya, sa'an nan Ya ce wa Malã'iku, "Shin, waɗannan kũ ne suka kasance sunã bauta wa?" info
التفاسير:

external-link copy
41 : 34

قَالُواْ سُبۡحَٰنَكَ أَنتَ وَلِيُّنَا مِن دُونِهِمۖ بَلۡ كَانُواْ يَعۡبُدُونَ ٱلۡجِنَّۖ أَكۡثَرُهُم بِهِم مُّؤۡمِنُونَ

Sukace: "Tsarki ya tabbata a gare Ka. Kai ne Majiɓincinmu, bã su ba. Ã'a, sun kasance sunã bauta wa aljannu. Mafi yawansu, da sũ suka yi ĩmani." info
التفاسير:

external-link copy
42 : 34

فَٱلۡيَوۡمَ لَا يَمۡلِكُ بَعۡضُكُمۡ لِبَعۡضٖ نَّفۡعٗا وَلَا ضَرّٗا وَنَقُولُ لِلَّذِينَ ظَلَمُواْ ذُوقُواْ عَذَابَ ٱلنَّارِ ٱلَّتِي كُنتُم بِهَا تُكَذِّبُونَ

Sabõda haka, a yau sãshenku bã ya mallakar wani amfãni ga wani sãshen, kuma bã ya mallakar wata cũta, kuma Munã cẽwa ga waɗanda suka yi zalunci, Ku ɗanɗani azabar wutã wadda "kuka kasance game da ita, kunã ƙaryatãwa." info
التفاسير:

external-link copy
43 : 34

وَإِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُنَا بَيِّنَٰتٖ قَالُواْ مَا هَٰذَآ إِلَّا رَجُلٞ يُرِيدُ أَن يَصُدَّكُمۡ عَمَّا كَانَ يَعۡبُدُ ءَابَآؤُكُمۡ وَقَالُواْ مَا هَٰذَآ إِلَّآ إِفۡكٞ مُّفۡتَرٗىۚ وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لِلۡحَقِّ لَمَّا جَآءَهُمۡ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ مُّبِينٞ

Kuma idan an karanta ãyõyin Mu bayyanannu a kansu, sai su ce: "Wannan bai zama ba fãce namiji ne yanã son ya kange ku daga abin da ubanninku suka kasance sunã bauta wa." Kuma su ce: "Wannan bai zama ba fãce ƙiren ƙarya da aka ƙãga." Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: ga gaskiya a lõkacin da ta je musu: "Wannan bã kõme ba fãce sihiri ne bayyananne." info
التفاسير:

external-link copy
44 : 34

وَمَآ ءَاتَيۡنَٰهُم مِّن كُتُبٖ يَدۡرُسُونَهَاۖ وَمَآ أَرۡسَلۡنَآ إِلَيۡهِمۡ قَبۡلَكَ مِن نَّذِيرٖ

Kuma ba Mu bã su waɗansu littattafai ba waɗanda suke karãtun su, kuma ba Mu aika wani mai gargaɗi ba zuwa gare su a gabãninka! info
التفاسير:

external-link copy
45 : 34

وَكَذَّبَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ وَمَا بَلَغُواْ مِعۡشَارَ مَآ ءَاتَيۡنَٰهُمۡ فَكَذَّبُواْ رُسُلِيۖ فَكَيۡفَ كَانَ نَكِيرِ

Kuma waɗanda suke a gabãninsu, sun ƙaryata, alhãli kuwa ba su kai ushurin-ushurin abin da Muka bã su ba, sai suka ƙaryata Manzanni Na! To, yãya musũ Na (ga maƙaryata) ya kasance? info
التفاسير:

external-link copy
46 : 34

۞ قُلۡ إِنَّمَآ أَعِظُكُم بِوَٰحِدَةٍۖ أَن تَقُومُواْ لِلَّهِ مَثۡنَىٰ وَفُرَٰدَىٰ ثُمَّ تَتَفَكَّرُواْۚ مَا بِصَاحِبِكُم مِّن جِنَّةٍۚ إِنۡ هُوَ إِلَّا نَذِيرٞ لَّكُم بَيۡنَ يَدَيۡ عَذَابٖ شَدِيدٖ

Ka ce: "Ina yi muku wa'azi ne kawai da kalma guda! watau ku tsayu dõmin Allah, bibbiyu da ɗaiɗai, sa'an nan ku yi tunãni, bãbu wata hauka ga ma'abũcinku. Shĩ bai zama ba fãce mai gargaɗi ne a gare ku a gaba ga wata azãba mai tsanani. info
التفاسير:

external-link copy
47 : 34

قُلۡ مَا سَأَلۡتُكُم مِّنۡ أَجۡرٖ فَهُوَ لَكُمۡۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَى ٱللَّهِۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدٞ

Ka ce: "Abin da na rõƙe ku na wani sakamako, to, amfãninsa nãku ne. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Allah, kuma shi Ma shadai ne a kan dukan kõme." info
التفاسير:

external-link copy
48 : 34

قُلۡ إِنَّ رَبِّي يَقۡذِفُ بِٱلۡحَقِّ عَلَّٰمُ ٱلۡغُيُوبِ

Ka ce: "Lalle Ubangijina Yanã jẽfa gaskiya. (Shi) Masanin abũbuwan fake ne." info
التفاسير: