Qurani Kərimin mənaca tərcüməsi - Hövsa dilinə tərcümə - Əbu Bəkir Cumi.

external-link copy
106 : 2

۞ مَا نَنسَخۡ مِنۡ ءَايَةٍ أَوۡ نُنسِهَا نَأۡتِ بِخَيۡرٖ مِّنۡهَآ أَوۡ مِثۡلِهَآۗ أَلَمۡ تَعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ

Abin da Muka shãfe* daga ãya, ko kuwa Muka jinkirtar da ita, zã Mu zo da mafi Alhẽri daga gare ta ko kuwa misãlinta. Ashe, ba ka sani ba, cẽwa lalle ne, Allah a kan dukkan kõme Mai ĩkon yi ne? info

* Wannan ãya da abin da yakea bayanta sunã kõrewar shubuhãtu watau rikice-rikicen addini da maƙiyan addini suke sanyãwa a cikinsa, dõmin su sanya Musulmi a cikin shakka da ruɗu.

التفاسير: