Qurani Kərimin mənaca tərcüməsi - Hövsa dilinə tərcümə - Əbu Bəkir Cumi.

Al'asr

external-link copy
1 : 103

وَٱلۡعَصۡرِ

Ina rantsuwa da zãmani.* info

* Wasu suna fassarawa da lokacin sallar La'asar da kuma marece. A kõwane dai, an bai wa lokaci muhimmanci, zãmani yana yanke wanda bai yanke shi ba. ba ya halatta ga mutum wata mudda ta zãmani ta wuce shi bai san amfãnin da ya sãma wa kansa a cikinta ba, kuma kõme ya sãmu idan ba addini ba ne, to, hasãrace.

التفاسير:

external-link copy
2 : 103

إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لَفِي خُسۡرٍ

Lalle ne mutum yana a cikin hasara. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 103

إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ وَتَوَاصَوۡاْ بِٱلۡحَقِّ وَتَوَاصَوۡاْ بِٱلصَّبۡرِ

Fãce waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi wa juna wasiyya da bin gaskiya, kuma suka yi wa juna wasiyya da yin haƙuri (su kam, basu cikin hasara). info
التفاسير: