* A nan hukunce-hukuncen alkawurra suka ƙãre a wannan sura daga ãyã ta sama da wannan. Kuma da wannan ãyã ta l09 Allah Yanã yi mana hikãyar abin da zai auku a Lãhira da bincinken Sa ga tsare alkawari, kõ rashin tsarewa. Ya fãra da Annabãwan Sa. Ya aiko, da ƙarin bãyani a kan irin muhãwarar da zã ta shiga a tsakãnin Sa da Annabãwa.Yã yi misãli da Ĩsã dõmin mutanensa nã nan a cikin wannan al'umma, anã kiran su zuwa ga musulunci, kuma domin shine Annabi na ƙarshen da ba a manta abubuwan da mutanensa suka yi ba a gabanin ɗauke shi ɗin.
* Hawãriyãwa su ne sahabban Ĩsã, amincin Allah ya tabbata a gare shi. Sunã sanyãwar farãren tufãfi, dõmin haka aka yi musu suna da haka.