ترجمة معاني القرآن الكريم - الترجمة الهوساوية - أبو بكر جومي

رقم الصفحة:close

external-link copy
78 : 5

لُعِنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۢ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ عَلَىٰ لِسَانِ دَاوُۥدَ وَعِيسَى ٱبۡنِ مَرۡيَمَۚ ذَٰلِكَ بِمَا عَصَواْ وَّكَانُواْ يَعۡتَدُونَ

An la'ani waɗanda suka kãfirta daga Banĩ Isrã'ĩla a kan harshen Dãwuda da Ĩsa ɗan Maryama. wannan kuwa sabõda sãɓãwar da suka yi ne, kuma sun kasance suna ta'addi.* info

* Ta'addi shĩ ne ƙetare iyãka da nufin zãlunci.

التفاسير:

external-link copy
79 : 5

كَانُواْ لَا يَتَنَاهَوۡنَ عَن مُّنكَرٖ فَعَلُوهُۚ لَبِئۡسَ مَا كَانُواْ يَفۡعَلُونَ

Sun kasance bã su hana juna daga abin ƙi, wanda suka aikata. Haƙĩƙa abin da suka kasance sunã aikatãwa yã munana. info
التفاسير:

external-link copy
80 : 5

تَرَىٰ كَثِيرٗا مِّنۡهُمۡ يَتَوَلَّوۡنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْۚ لَبِئۡسَ مَا قَدَّمَتۡ لَهُمۡ أَنفُسُهُمۡ أَن سَخِطَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡ وَفِي ٱلۡعَذَابِ هُمۡ خَٰلِدُونَ

Kana ganin mãsu yawa daga gare su, sunã jiɓintar waɗanda suka kãfirta. Haƙĩƙa tir da abin da rãyukansu suka gabãtar sabõda su, watau Allah Yã yi fushi da su, kuma a cikin azãba su mãsu dawwama ne info
التفاسير:

external-link copy
81 : 5

وَلَوۡ كَانُواْ يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلنَّبِيِّ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِ مَا ٱتَّخَذُوهُمۡ أَوۡلِيَآءَ وَلَٰكِنَّ كَثِيرٗا مِّنۡهُمۡ فَٰسِقُونَ

Kuma dã sun kasance sunã ĩmãni da Allah da Annabi da abin da aka saukar zuwa gare shi, dã ba su riƙe su masõya ba. Kuma amma mãsu yawa daga gare su, fãsiƙai ne. info
التفاسير:

external-link copy
82 : 5

۞ لَتَجِدَنَّ أَشَدَّ ٱلنَّاسِ عَدَٰوَةٗ لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱلۡيَهُودَ وَٱلَّذِينَ أَشۡرَكُواْۖ وَلَتَجِدَنَّ أَقۡرَبَهُم مَّوَدَّةٗ لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّا نَصَٰرَىٰۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّ مِنۡهُمۡ قِسِّيسِينَ وَرُهۡبَانٗا وَأَنَّهُمۡ لَا يَسۡتَكۡبِرُونَ

Lalle ne kana sãmun mafiya tsananin mutãne a adãwa ga waɗanda suka yi ĩmãni, Yahudu ne da waɗanda suka yi shirki. Kuma lalle ne kanã sãmun mafiya kusantarsu a sõyayya ga waɗanda suka yi ĩmãni su ne waɗanda suka ce: "Lalle mu ne Nasãra." Wancan kuwa sabõda akwai ¡issawa da ruhubãnãwa* daga cikinsu. Kuma lalle ne su, bã su yin girman kai. info

* Ƙissĩsi shĩ ne lĩmãnin kiristãwa, ruhubãnanci shĩ ne mutum ya tsabbace daga mutãne dõmin ibãda, kuma ba ya yin aure. Baruhubãne guda, ruhubãnãwa jam'i.

التفاسير:

external-link copy
83 : 5

وَإِذَا سَمِعُواْ مَآ أُنزِلَ إِلَى ٱلرَّسُولِ تَرَىٰٓ أَعۡيُنَهُمۡ تَفِيضُ مِنَ ٱلدَّمۡعِ مِمَّا عَرَفُواْ مِنَ ٱلۡحَقِّۖ يَقُولُونَ رَبَّنَآ ءَامَنَّا فَٱكۡتُبۡنَا مَعَ ٱلشَّٰهِدِينَ

Kuma idan suka ji abin da aka saukar zuwa ga Manzo, kanã ganin idanunsu sunã zubar da hawãye, sabõda abin da suka sani daga gaskiya, sunã cewa: "Yã Ubangijinmu! Mun yi ĩmãni, sai ka rubuta mu tãre da mãsu shaida. info
التفاسير: