* Kwanukan Allah, sũ ne masĩfu waɗanda ke sãmun kãfirai waɗanda bã su bin sharĩ'ar Allah. Wãtau Allah Ya umurci Annabi ya gaya wa Musulmi, cewa wanda bã ya tsõron masĩfu sabõda ya ki aiwatar da sharĩ'ar Allah a kansa to kada Musulmi su dãmu da shi, watau kãfiran amãna nã iya bin dõkõkinsu na al'ãda, bãbu ruwan Musulmi matuƙar dai ba su shũka wata fitina ba a gare su. A bãyan haka Allah zai sãka wa kõwa game da aikinsa.
* Bã Musulmi kawai aka aikowa Manzo ba,ba su kawai aka bã su sharĩ'a ba, kuma aka umurce su da binta ba, Banĩ Isrã'ĩla ma an bã su haka kuma sunɗaukaka a kan mutãne a lõkacin da suka yi aiki da sharĩ'ar, kuma suka ƙasƙanta a lõkacin da suka bar aiki da ita. Musulmi ma haka suke idan sun bar sharĩ'ar da Allah Ya aza su a kanta, zã su ƙasƙanta yadda Yahũdawa suka ƙasƙanta.