Kuma da sãɓawar dare da yini da abin da Allah Ya saukar daga sama na arziki, sa'an nan Ya rãyar da ƙasa game da shi a bãyan mutuwarta, da jũyawar iskõki, akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin hankali.
Gaba gare su (a Lãhira) akwai Jahannama, kuma abin da suka sanã'anta bã ya wadãtar da su daga kõme, kuma abũbuwan da suka riƙa majiɓinta, baicin Allah, bã su wãdatar da su daga kõme. Kuma sunã da wata azãba mai girma.
Kuma Ya hõre muku abin da ke a cikin sammai da abin da ke a cikin ƙasa, gabã ɗaya daga gare Shi yake. Lalle ne, a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin tunãni.