* A farkon Musulunci hijira sharaɗi ce ga shiga cikin waliccin Musulmi, amma bãyan da Musulunci ya yi ƙarfi, hijira ba ta zama sharaɗi ba, sai dai tanã wajaba ga Musulmi ya tashi daga inda bã ya iya tsare addininsa zuwa ga inda yake iya tsare shi, matuƙar bãbu wata wahala mai tsanani. Ana taimakon Musulmin da bai yi hijira ba ga abin da bai shãfi warware alkawarin Musulmi ba.
* Walicci shi ne kusanta da lizimtar wajabcin taimakon jũna.A farkon Musulunci, Musulmi bã su da walicci a kan wani Musulmi, sai idan yã yi hijira zuwa Madĩna. Bãyan cin Makka da wãtsuwar Musulunci sai waliccin Musulmi ya wajaba a kan kõwane Musulmi a inda duk yake, a cikin dũniya, gwargwadon hãli, amma kuma a cikin haka mafi kusantar zumuntã shi ne mafi cancanta da waliccin kõwane Musulmi, har dai ga abin da ya shãfi hãlãye na zaman mutum kamar aure da gãdo, da sauransu, kamar yadda littattafan sunna suka bayyana, a can cikin bãbin walicci.