* Mai gaskiya idan marasa gaskiya sun tãru sunã faɗa da shi, to, rashin jituwar tsakãninsu zai sanya Allah Ya kange shi daga sharrinsu, sũ duka, kamar husumar da ke tsakãnin Yahũdu da Nasãra da kuma tsakãnin sũ mushirikai, su duka mãsu yãƙi da Musulmi ne kuma mãsu sãɓãwa jũnã ne wajen aƙidõjinsu.
* Misãlin sãɓãni tsakãninsu; Nasãra suka taimaki Bukhta Nassara ga ɓata masallacin Baitil Maƙdis da jefa mũshe da shãra a ciki, dõmin ƙin Yahũdu. Wannan ƙiyayya tã bayyana har a cikin takardar alƙawari a tsakãnin Nasãra da Halifa Umar bn Khattãb suka ce kada ya bar Yahũdu su shiga Baitil Maƙdis. Sabõda haka idan wasu sun hana ku isa ga masallacinku kõ kuma suka jũyarda ku daga Alƙibla, to, kada ku ji kõme, sun yi irin aikin danginsu. Gabas da yamma na Allah ɗaya ne, duk inda aka jũyar da ku, to, a can yardar Allah take. A lõkacin Musulmi na dũbin Baitil Maƙdis ga salla a bãyan Hijira daga Makka, bã su son haka.
* Misãli na biyu Yahũdu na cewa Uzairu ɗãn Allah, kuma Nasãra sunã cewa Ĩsa ɗan Allah, Lãrabãwa na cewa Malã'iku 'ya'yan Allah. Wannan zai hana su jituwa har adãwarsu ga Musulmi ta yi tãsĩri.
* Misãli ne ga irin rikicin mushirikai ga addini kuma da yadda suka yi kamã da Yahũdu, waɗanda suka ce wa Mũsã: "Ka nũna mana Allah bayyane.".