የቅዱስ ቁርዓን ይዘት ትርጉም - የሀውሳ ቋንቋ ትርጉም - አቡበከር ጉሚ

የገፅ ቁጥር:close

external-link copy
87 : 17

إِلَّا رَحۡمَةٗ مِّن رَّبِّكَۚ إِنَّ فَضۡلَهُۥ كَانَ عَلَيۡكَ كَبِيرٗا

Fãce da rahama daga Ubangijinka. Lalle ne falalarSa ta kasance mai girma a kanka. info
التفاسير:

external-link copy
88 : 17

قُل لَّئِنِ ٱجۡتَمَعَتِ ٱلۡإِنسُ وَٱلۡجِنُّ عَلَىٰٓ أَن يَأۡتُواْ بِمِثۡلِ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ لَا يَأۡتُونَ بِمِثۡلِهِۦ وَلَوۡ كَانَ بَعۡضُهُمۡ لِبَعۡضٖ ظَهِيرٗا

Ka ce: "Lalle ne idan mutãne da aljannu sun tãru a kan su zo da misãlin wannan Alƙur'ãni bã zã su zo da misãlinsa ba, kuma kõ dã sãshinsu yã kasance, mataimaki ga sãshi." info
التفاسير:

external-link copy
89 : 17

وَلَقَدۡ صَرَّفۡنَا لِلنَّاسِ فِي هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ مِن كُلِّ مَثَلٖ فَأَبَىٰٓ أَكۡثَرُ ٱلنَّاسِ إِلَّا كُفُورٗا

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun caccanza dõmin mutãne, a cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane misãli sai mafi yawan mutãne suka ƙi (kõme) fãce kãfirci, info
التفاسير:

external-link copy
90 : 17

وَقَالُواْ لَن نُّؤۡمِنَ لَكَ حَتَّىٰ تَفۡجُرَ لَنَا مِنَ ٱلۡأَرۡضِ يَنۢبُوعًا

Kuma suka ce: "Bã zã mu yi ĩmãni ba dõminka sai kã ɓuɓɓugar* da idan ruwa daga ƙasa. info

* Kãfiri bã ya iya hangen abinda bã a iya taɓa shi da gaɓoɓin ji na jiki, dõmin haka suka nemi ɗayan waɗannan abũbuwa ya auku kãmin su yi ĩmãni. Mũmini yanã kange da ganin basĩra, dõmin haka ya wadãtu da zaman Alƙur'ani ãyã mai isa ga ya yi ĩmãni da shi.

التفاسير:

external-link copy
91 : 17

أَوۡ تَكُونَ لَكَ جَنَّةٞ مِّن نَّخِيلٖ وَعِنَبٖ فَتُفَجِّرَ ٱلۡأَنۡهَٰرَ خِلَٰلَهَا تَفۡجِيرًا

"Kõ kuma wata gõna daga dabĩnai da inabi ta kasance a gare ka. Sa'an nan ka ɓuɓɓugar da ƙõramu a tsakãninta ɓuɓɓugarwa." info
التفاسير:

external-link copy
92 : 17

أَوۡ تُسۡقِطَ ٱلسَّمَآءَ كَمَا زَعَمۡتَ عَلَيۡنَا كِسَفًا أَوۡ تَأۡتِيَ بِٱللَّهِ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةِ قَبِيلًا

"Kõ kuwa ka kãyar da sama a kanmu kaɓukka kõ kuwa ka zo da Allah, da malã'iku banga-banga." info
التفاسير:

external-link copy
93 : 17

أَوۡ يَكُونَ لَكَ بَيۡتٞ مِّن زُخۡرُفٍ أَوۡ تَرۡقَىٰ فِي ٱلسَّمَآءِ وَلَن نُّؤۡمِنَ لِرُقِيِّكَ حَتَّىٰ تُنَزِّلَ عَلَيۡنَا كِتَٰبٗا نَّقۡرَؤُهُۥۗ قُلۡ سُبۡحَانَ رَبِّي هَلۡ كُنتُ إِلَّا بَشَرٗا رَّسُولٗا

"Kõ kuwa wani gida na zĩnãriya ya kasance a gare ka, kõ kuwa ka tãka a cikin sama. Kuma bã zã mu yi ĩmãni ba ga tãkawarka, sai ka sassaukõ da wani littãfi a kanmu, munã karantã shi." Ka ce: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijĩna! Ban kasance ba fãce mutum, Manzo." info
التفاسير:

external-link copy
94 : 17

وَمَا مَنَعَ ٱلنَّاسَ أَن يُؤۡمِنُوٓاْ إِذۡ جَآءَهُمُ ٱلۡهُدَىٰٓ إِلَّآ أَن قَالُوٓاْ أَبَعَثَ ٱللَّهُ بَشَرٗا رَّسُولٗا

Kuma bãbu abin da ya hana mutãne su yi ĩmãni, a lõkacin da shiriya ta jẽ musu, fãce sunce, "Shin, Allah zai aiko mutum ya zamo yana Manzo." info
التفاسير:

external-link copy
95 : 17

قُل لَّوۡ كَانَ فِي ٱلۡأَرۡضِ مَلَٰٓئِكَةٞ يَمۡشُونَ مُطۡمَئِنِّينَ لَنَزَّلۡنَا عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ مَلَكٗا رَّسُولٗا

Ka ce: "Dã malã'iku sun kasance a cikin ƙasa, kuma sunã tafiya, sunã masu natsuwa, lalle ne dã mun saukar da malã'ika daga sama ya zama manzo a kansu." info
التفاسير:

external-link copy
96 : 17

قُلۡ كَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدَۢا بَيۡنِي وَبَيۡنَكُمۡۚ إِنَّهُۥ كَانَ بِعِبَادِهِۦ خَبِيرَۢا بَصِيرٗا

Ka ce: "Allah Yã isa zama shaida a tsakãnina da ku. Lalle Shi Ya kasance ga bãyinsa, mai ƙididdigewa ne Mai gani." info
التفاسير: