የቅዱስ ቁርዓን ይዘት ትርጉም - የሀውሳ ቋንቋ ትርጉም - አቡበከር ጉሚ

Alhijr

external-link copy
1 : 15

الٓرۚ تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِ وَقُرۡءَانٖ مُّبِينٖ

A. L̃.R. Waɗan can ãyoyin littãfi ne da abin karantãwa mai bayyanãwa. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 15

رُّبَمَا يَوَدُّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوۡ كَانُواْ مُسۡلِمِينَ

Da yawa waɗanda suka kãfirta suke gũrin dã dai sun kasance Musulmi.* info

* Kõwane kãfiri yanã gũrin yã zama Musulmi dõmin abin da yake gani na shiriya da ladubban Musulunci, waɗanda ya tabbata bãbu zama lãfiya ga mutum fãce idan yã sãme su, amma shaiɗan yanã hana shi musulunta sabõda waɗansu dalĩlai da yake sanyãwa a ganinsa.

التفاسير:

external-link copy
3 : 15

ذَرۡهُمۡ يَأۡكُلُواْ وَيَتَمَتَّعُواْ وَيُلۡهِهِمُ ٱلۡأَمَلُۖ فَسَوۡفَ يَعۡلَمُونَ

Ka bar su su ci kuma su ji dãdi, kuma gũri ya shagaltar da su, sa'an nan da sannu zã su sani. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 15

وَمَآ أَهۡلَكۡنَا مِن قَرۡيَةٍ إِلَّا وَلَهَا كِتَابٞ مَّعۡلُومٞ

Kuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da littafi sananne. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 15

مَّا تَسۡبِقُ مِنۡ أُمَّةٍ أَجَلَهَا وَمَا يَسۡتَـٔۡخِرُونَ

Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 15

وَقَالُواْ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِي نُزِّلَ عَلَيۡهِ ٱلذِّكۡرُ إِنَّكَ لَمَجۡنُونٞ

Suka ce: "Yã kai wanda aka saukar da Ambato (Alƙur'ãni) a kansa! Lalle ne kai, haƙĩƙa, mahaukaci ne." info
التفاسير:

external-link copy
7 : 15

لَّوۡمَا تَأۡتِينَا بِٱلۡمَلَٰٓئِكَةِ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ

"Dõmin me bã zã ka zo mana da malã'ĩku ba idan ka kasance daga mãsu gaskiya?" info
التفاسير:

external-link copy
8 : 15

مَا نُنَزِّلُ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةَ إِلَّا بِٱلۡحَقِّ وَمَا كَانُوٓاْ إِذٗا مُّنظَرِينَ

Bã Mu sassaukar da malã'iku fãce da gaskiya,* bã zã su kasance, a wannan lõkacin, waɗanda ake yi wa jinkĩri ba. info

* Gaskiya a nan anã nufin azãba dõmin zuwanta tabbatacce ne. Dukan abin da yake tabbatacce shĩ ne haƙƙun, watau gaskiya.

التفاسير:

external-link copy
9 : 15

إِنَّا نَحۡنُ نَزَّلۡنَا ٱلذِّكۡرَ وَإِنَّا لَهُۥ لَحَٰفِظُونَ

Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur'ãni), kuma lale Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayẽwane gare shi. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 15

وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ فِي شِيَعِ ٱلۡأَوَّلِينَ

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Manzanni a cikin ƙungiyõyin farko, gabãnin ka. info
التفاسير:

external-link copy
11 : 15

وَمَا يَأۡتِيهِم مِّن رَّسُولٍ إِلَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ

Kuma wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu, izgili a gare shi. info
التفاسير:

external-link copy
12 : 15

كَذَٰلِكَ نَسۡلُكُهُۥ فِي قُلُوبِ ٱلۡمُجۡرِمِينَ

Kamar wancan ne Muke shigar da shi* a cikin zukãtan mãsu laifi. info

* Shirki da kãfirci da ƙaryatãwa, su duka izgili ne da addini.

التفاسير:

external-link copy
13 : 15

لَا يُؤۡمِنُونَ بِهِۦ وَقَدۡ خَلَتۡ سُنَّةُ ٱلۡأَوَّلِينَ

Bã su yin ĩmãni da shi,(4( kuma haƙĩƙa, hanyar mutãnen farko ta shige. info

* Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Hanyar mutãnen farko ta ƙaryata Manzanni har a lõkacin da Allah zai halaka su da azãbarsa.

التفاسير:

external-link copy
14 : 15

وَلَوۡ فَتَحۡنَا عَلَيۡهِم بَابٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ فَظَلُّواْ فِيهِ يَعۡرُجُونَ

Kuma dã Mun bũɗe wata ƙõfa daga sama a kansu har suka wuni a ciki sunã tãkãwa. info
التفاسير:

external-link copy
15 : 15

لَقَالُوٓاْ إِنَّمَا سُكِّرَتۡ أَبۡصَٰرُنَا بَلۡ نَحۡنُ قَوۡمٞ مَّسۡحُورُونَ

Lalle ne dã sun ce: "Abin sani kawai, an rufe idãnuwanmu ne. Ã'a, mũ mutãne ne waɗanda aka sihirce." info
التفاسير: