Қуръони Карим маъноларининг таржимаси - Ҳавсача таржима - Абу Бакр Жуми

Al'shams

external-link copy
1 : 91

وَٱلشَّمۡسِ وَضُحَىٰهَا

Ina rantsuwa da rãnã da hantsinta. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 91

وَٱلۡقَمَرِ إِذَا تَلَىٰهَا

Kuma da wata idan ya bi ta. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 91

وَٱلنَّهَارِ إِذَا جَلَّىٰهَا

Da yini a lõkacin da ya bayyana ta. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 91

وَٱلَّيۡلِ إِذَا يَغۡشَىٰهَا

Da dare a lõkacin da ya ke rufe ta. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 91

وَٱلسَّمَآءِ وَمَا بَنَىٰهَا

Da sama da abin da ya gina ta. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 91

وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا طَحَىٰهَا

Da ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 91

وَنَفۡسٖ وَمَا سَوَّىٰهَا

Da rai da abin da ya daidaita shi. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 91

فَأَلۡهَمَهَا فُجُورَهَا وَتَقۡوَىٰهَا

Sa'an nan ya yi masa Ilhamar fãjircinsa da shiryuwarsa. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 91

قَدۡ أَفۡلَحَ مَن زَكَّىٰهَا

Lalle ne wanda ya tsarkake* shi (rai) ya sãmi babban rabo. info

* Karɓar imãni da aiki da abinda ya ƙunsa tsarkake rai ne.

التفاسير:

external-link copy
10 : 91

وَقَدۡ خَابَ مَن دَسَّىٰهَا

Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe* shi (da laifi) ya tãɓe. info

* Kãfirci turbuɗe rai ne da zunubi.

التفاسير:

external-link copy
11 : 91

كَذَّبَتۡ ثَمُودُ بِطَغۡوَىٰهَآ

Samũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu. info
التفاسير:

external-link copy
12 : 91

إِذِ ٱنۢبَعَثَ أَشۡقَىٰهَا

A lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu). info
التفاسير:

external-link copy
13 : 91

فَقَالَ لَهُمۡ رَسُولُ ٱللَّهِ نَاقَةَ ٱللَّهِ وَسُقۡيَٰهَا

Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta!" info
التفاسير:

external-link copy
14 : 91

فَكَذَّبُوهُ فَعَقَرُوهَا فَدَمۡدَمَ عَلَيۡهِمۡ رَبُّهُم بِذَنۢبِهِمۡ فَسَوَّىٰهَا

Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi). info
التفاسير:

external-link copy
15 : 91

وَلَا يَخَافُ عُقۡبَٰهَا

Kuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar). info
التفاسير: