* Aikata ƙaramin laifi yana sabbaba babban laifi har ɓarna mai yawa ta wãtsu a cikin ƙasa.
* Muhãrib shi ne ɗan fashi mai tare hanya da makamai. Ana yi masa ɗayan abin da aka ga yã dãce da shi. Wanda aka yi wa "Salbu" sai kuma a kashe shi. Amfanin Salbu shi ne a gan shi, dõmin hankalin mutãne ya natsu. Korewa yanzu sai ta koma ga ɗauri har ya mutu ko ya tuba.
* Wasĩla ita ce dukkan aikin ibãda wanda zai kusantar da mutum zuwa ga Ubangijinsa, amma da sharaɗin an gina shi a kan taƙawa. Kuma taƙawa ita ce bin Allah kamar yadda Ya yi umurni a bi Shi, ta hanyar manzon Sa kawai. Jihãdi yana cikin taƙawa amma Yã kõma ambatonsa ne domin muhimmancinsa. Shi kuma iri biyu ne: ƙararmi, watau yãƙin abokan gãbã na bayyane, da babba, shi ne yãƙin abokan gãbã na ɓoye, watau rai da shaiɗan. Wanda maƙiyinsa na bayyane ya kashe shi yã mutu shahĩdi, wanda maƙiyinsa na ɓoye ya kashe shĩ ya mutu fãsiƙi ko kãfiri watau shaƙiyyi.