Қуръони Карим маъноларининг таржимаси - Ҳавсача таржима - Абу Бакр Жуми

Бет рақами:close

external-link copy
34 : 14

وَءَاتَىٰكُم مِّن كُلِّ مَا سَأَلۡتُمُوهُۚ وَإِن تَعُدُّواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ لَا تُحۡصُوهَآۗ إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لَظَلُومٞ كَفَّارٞ

Kuma Ya bã ku dukkan abin da kuka rõƙe Shi kuma idan kun ƙidaya, ni'imar Allah bã zã ku lissafe ta ba. Lalle ne mutum, haƙĩƙa, mai yawan zãlunci ne, mai yawan kãfirci. info
التفاسير:

external-link copy
35 : 14

وَإِذۡ قَالَ إِبۡرَٰهِيمُ رَبِّ ٱجۡعَلۡ هَٰذَا ٱلۡبَلَدَ ءَامِنٗا وَٱجۡنُبۡنِي وَبَنِيَّ أَن نَّعۡبُدَ ٱلۡأَصۡنَامَ

Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Yã Ubangijina! Ka sanyã wannan gari* amintacce kuma Ka nĩsanta ni, nĩ da ɗiyãna daga bauta wa gumãka. info

* Wannan gari watau Makka. Anã tunãtar da Lãrabãwa ga kãkansu Ibrãhĩm da addu'ar da ya yi sabõda garin Makka da mutãnen garin da ɗiyan Ismã'ila dõmin su wa'aztu.

التفاسير:

external-link copy
36 : 14

رَبِّ إِنَّهُنَّ أَضۡلَلۡنَ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلنَّاسِۖ فَمَن تَبِعَنِي فَإِنَّهُۥ مِنِّيۖ وَمَنۡ عَصَانِي فَإِنَّكَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

"Yã Ubangijina! Lalle ne sũ, sun ɓatar da mãsu yawa daga mutãne sa'an nan wanda ya bĩ ni, to, lalle shi, yanã daga gare ni, kuma wanda ya sãɓa mini, to, lalle ne Kai Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. info
التفاسير:

external-link copy
37 : 14

رَّبَّنَآ إِنِّيٓ أَسۡكَنتُ مِن ذُرِّيَّتِي بِوَادٍ غَيۡرِ ذِي زَرۡعٍ عِندَ بَيۡتِكَ ٱلۡمُحَرَّمِ رَبَّنَا لِيُقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ فَٱجۡعَلۡ أَفۡـِٔدَةٗ مِّنَ ٱلنَّاسِ تَهۡوِيٓ إِلَيۡهِمۡ وَٱرۡزُقۡهُم مِّنَ ٱلثَّمَرَٰتِ لَعَلَّهُمۡ يَشۡكُرُونَ

"Yã Ubangijinmu! Lalle ne ni, na zaunar da zuriyata ga rãfi wanda ba ma'abũcin shũka ba, a wurin ¦ãkinka mai alfarma. Yã Ubangijinmu! Dõmin su tsayar da salla. Sai Ka sanya zukãta daga mutãne sunã gaggãwar bẽgenzuwa gare su, kuma ka azurtã su daga 'ya'yan itãce, mai yiwuwã ne sunã gõdẽwã." info
التفاسير:

external-link copy
38 : 14

رَبَّنَآ إِنَّكَ تَعۡلَمُ مَا نُخۡفِي وَمَا نُعۡلِنُۗ وَمَا يَخۡفَىٰ عَلَى ٱللَّهِ مِن شَيۡءٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا فِي ٱلسَّمَآءِ

"Yã Ubangijinmu! Lalle ne Kai Kanã sanin abin da muke ɓõyẽwa, da abin da muke bayyanãwa. Kuma bãbu abin da yake ɓõyẽwa ga Alah, daga wani abu a cikin ƙasa, kuma bãbu a cikin sama." info
التفاسير:

external-link copy
39 : 14

ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي وَهَبَ لِي عَلَى ٱلۡكِبَرِ إِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَۚ إِنَّ رَبِّي لَسَمِيعُ ٱلدُّعَآءِ

"Gõdiyã ta tabbata ga Allah wanda Yake Ya bã ni inã a cikin tsufa Ismã'ila da Is'hãƙa. Lalle ne Ubangijina, haƙĩƙa, Mai jin addu'a ne." info
التفاسير:

external-link copy
40 : 14

رَبِّ ٱجۡعَلۡنِي مُقِيمَ ٱلصَّلَوٰةِ وَمِن ذُرِّيَّتِيۚ رَبَّنَا وَتَقَبَّلۡ دُعَآءِ

"Yã Ubangijina! Ka sanyã ni mai tsayar da salla. Kuma daga zũriyyata. Yã Ubangijinmu! Kuma Ka karɓi addu'ata." info
التفاسير:

external-link copy
41 : 14

رَبَّنَا ٱغۡفِرۡ لِي وَلِوَٰلِدَيَّ وَلِلۡمُؤۡمِنِينَ يَوۡمَ يَقُومُ ٱلۡحِسَابُ

"Yã Ubangijinmu! Ka yi gãfara gare ni, kuma ga mahaifãna, kuma da mũminai, a rãnar da hisãbi yake tsayãwa." info
التفاسير:

external-link copy
42 : 14

وَلَا تَحۡسَبَنَّ ٱللَّهَ غَٰفِلًا عَمَّا يَعۡمَلُ ٱلظَّٰلِمُونَۚ إِنَّمَا يُؤَخِّرُهُمۡ لِيَوۡمٖ تَشۡخَصُ فِيهِ ٱلۡأَبۡصَٰرُ

"Kuma kada ka yi zaton Allah Mai shagalã ne daga abin da azzalumai suke aikatãwã. Abin sani kawai, Yanã jinkirta musu ne zuwa ga wani wuni, wanda idãnuwa suke fita turu- turu a cikinsa." info
التفاسير: