* Suka cire rĩgarsa, suka jefa shi da gũga a cikin rĩjiya. Sa'an nan suka sanya wa rigarsa jinin wata dabba da suka yanka, dõmin ya zama alãmar cewa kerkeci ya cinye Yũsufu. Gã rĩgarsa ta ɓãci da jinin jikinsa, watau jinin shĩ ne alãmar yã mutu. Sai suka manta cewa kãfin kerkeci ya cinye yãro a cikin rĩgarsa, sai yã kekketa rĩgar tukun.
* Muhãwararsu tãre da ubansu.Yã nũna baƙin ciki, amma kuma ya mayar da al'amari ga Allah.
* Ãyari ya je kusa da rĩjiyar Yũsufu, har suka kãma shi ya zama bãwa abin sayarwa a hannunsu.
* Ãyarin, sun tafi da shi, sun sayar da shi a kan kuɗi kaɗan, dõmin sun sani, shĩ bã bãwansu ba ne, tsintõ shi suka yi. Sabõda haka kõme suka sãmu game da shi, rĩba ce a gare su. Kuma gudun kada iyãyensa su gãne shi, su rasa kõme daga gare shi gabã ɗaya.
* Yũsufu a gidan sarauta, kuma a cikin hãlin girma da ɗaukaka. Gidan Azĩzĩ Masar, watau firãyim Minista, babban wazĩrin Masar.