* Saukar da Alƙur'ãni a cikin shekaru ashirin ko ashirin da uku ya yi kama da saukar ãyõyin Mũsã tãre a lõkacin da yake kiran Fir'auna zuwa ga addini.
* Muƙãranar yin ĩmãni da rashin ĩmãnin mutãne ga Alƙur'ãni ba zai rage gaskiyarsa da kõme ba, sai dai waɗanda suka ƙi ĩmãnin ne zã su cũtu, sa'an nan da bambanci a tsakãnin mai ilmi da jãhili. Mai ilmi yanã da sauƙin jãwuwa zuwa ga gaskiya har ya rasa abin da zai aikata fãce ya fãɗi rikice, a kan haɓarsa, yanã mayar da al'amari ga Allah kuma yanã tawali'u.
* Muƙarana a tsakãnin sũnayen Allah waɗanda ake kiran sa da su wajen rõƙo da waɗanda bã a yin roko da su. Sũnãyen mafiya kyau da ake kiran Allah da su Hadĩsi ya kãwo su sai a nħma daga Jalãlaini.** Kuma tsakaitãwa wajen karãtun salla ko addu'a kamar yadda aikin Annabi ya nũna yadda ake yi, kada a bayyana kada a ɓõye. Sai dai tsaka.
* Ka ce: "Allah ba Shi da abõkin muƙãrana a kõwace jiha. Shi kaɗai Ya cancanci girmamãwa." Sabõda haka ka girmama Shi, girmãmãwar da ta dãce da Shi.