قرآن کریم کے معانی کا ترجمہ - ہاؤسا ترجمہ - ابو بکر جومی

Al'qari'ah

external-link copy
1 : 101

ٱلۡقَارِعَةُ

Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)! info
التفاسير:

external-link copy
2 : 101

مَا ٱلۡقَارِعَةُ

Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa? info
التفاسير:

external-link copy
3 : 101

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلۡقَارِعَةُ

Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa? info
التفاسير:

external-link copy
4 : 101

يَوۡمَ يَكُونُ ٱلنَّاسُ كَٱلۡفَرَاشِ ٱلۡمَبۡثُوثِ

Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 101

وَتَكُونُ ٱلۡجِبَالُ كَٱلۡعِهۡنِ ٱلۡمَنفُوشِ

Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 101

فَأَمَّا مَن ثَقُلَتۡ مَوَٰزِينُهُۥ

To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 101

فَهُوَ فِي عِيشَةٖ رَّاضِيَةٖ

To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 101

وَأَمَّا مَنۡ خَفَّتۡ مَوَٰزِينُهُۥ

Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi). info
التفاسير:

external-link copy
9 : 101

فَأُمُّهُۥ هَاوِيَةٞ

To, uwarsa Hãwiya ce. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 101

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا هِيَهۡ

Kuma me ya sanar da kai mece ce ita? info
التفاسير:

external-link copy
11 : 101

نَارٌ حَامِيَةُۢ

Wata wuta ce mai kuna. info
التفاسير: