قۇرئان كەرىم مەنىلىرىنىڭ تەرجىمىسى - ھۇساچە تەرجىمىسى- ئەبۇبەكرى جومىي

بەت نومۇرى:close

external-link copy
50 : 40

قَالُوٓاْ أَوَلَمۡ تَكُ تَأۡتِيكُمۡ رُسُلُكُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِۖ قَالُواْ بَلَىٰۚ قَالُواْ فَٱدۡعُواْۗ وَمَا دُعَٰٓؤُاْ ٱلۡكَٰفِرِينَ إِلَّا فِي ضَلَٰلٍ

Suka ce: "Ashe, Manzanninku ba su jẽ muku da hujjõji bayyanannu ba?" Suka ce: "Na'am, sun jẽ!" Suka ce: "To, ku rõƙa." Kuma rõƙon kãfirai bai zamo ba fãce a cikin ɓata. info
التفاسير:

external-link copy
51 : 40

إِنَّا لَنَنصُرُ رُسُلَنَا وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَيَوۡمَ يَقُومُ ٱلۡأَشۡهَٰدُ

Lalle Mũ, hakĩka, Munã taimakon ManzanninMu da waɗanda suka yi ĩmãni, a cikin rãyuwar dũniya da rãnar da shaidu ke tsayãwa. info
التفاسير:

external-link copy
52 : 40

يَوۡمَ لَا يَنفَعُ ٱلظَّٰلِمِينَ مَعۡذِرَتُهُمۡۖ وَلَهُمُ ٱللَّعۡنَةُ وَلَهُمۡ سُوٓءُ ٱلدَّارِ

Rãnar da uzurin azzãlumai bã ya amfãninsu, kuma sunã da la'ana, kuma sunã da mũnin gida. info
التفاسير:

external-link copy
53 : 40

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡهُدَىٰ وَأَوۡرَثۡنَا بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ ٱلۡكِتَٰبَ

Kuma lalle haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã shiriya, kuma Mun gãdar da Banĩ Isrã'ĩla Littãfi. info
التفاسير:

external-link copy
54 : 40

هُدٗى وَذِكۡرَىٰ لِأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِ

Shiryarwa da tunãwa ga ma'abũta hankali. info
التفاسير:

external-link copy
55 : 40

فَٱصۡبِرۡ إِنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لِذَنۢبِكَ وَسَبِّحۡ بِحَمۡدِ رَبِّكَ بِٱلۡعَشِيِّ وَٱلۡإِبۡكَٰرِ

Sabõda haka, ka yi haƙuri, lalle wa'adin Allah gaskiya ne. Kuma ka nẽmi gãfara ga zunubinka, kuma ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, maraice da kuma wãyẽwar sãfiya. info
التفاسير:

external-link copy
56 : 40

إِنَّ ٱلَّذِينَ يُجَٰدِلُونَ فِيٓ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ بِغَيۡرِ سُلۡطَٰنٍ أَتَىٰهُمۡ إِن فِي صُدُورِهِمۡ إِلَّا كِبۡرٞ مَّا هُم بِبَٰلِغِيهِۚ فَٱسۡتَعِذۡ بِٱللَّهِۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡبَصِيرُ

Lalle waɗanda ke jãyayya a cikin ãyõyin Allah, bã game da wani dalĩli wanda ya jẽ musu ba, bãbu kõme a cikin kirãzansu, fãce girman kai, ba su zama mãsu isa ga gũrinsu ba, sabõda haka ka nẽmi tsari daga Allah. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai ji, Mai gani. info
التفاسير:

external-link copy
57 : 40

لَخَلۡقُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ أَكۡبَرُ مِنۡ خَلۡقِ ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ

Lalle halittar sammai da ƙasã, ita ce mafi girma daga halittar mutãne, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba. info
التفاسير:

external-link copy
58 : 40

وَمَا يَسۡتَوِي ٱلۡأَعۡمَىٰ وَٱلۡبَصِيرُ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ وَلَا ٱلۡمُسِيٓءُۚ قَلِيلٗا مَّا تَتَذَكَّرُونَ

Kuma makãho da mai gani bã su daidaita kuma waɗanda suka yi ĩmãni suka, aikata ayyukan ƙwarai da mai mũnanãwa bã su daidaita. Kaɗan ƙwarai, kuke yin tunãni. info
التفاسير: