* Yin addini ɗabĩ'a ce wadda Allah Ya halicci mutum akanta. Idan mutum ya bi abin da Allah Ya umurce shi da yi kõ bari, to yã yi addinin gaskiya, idan kuwa bai yi haka ba, ya zama mushiriki game da wanda yake karɓar umurni daga gare shi.
* Ya fassara mushirikai da ãyã ta 32. Wannan ya nũna ta yi nũni ga hana dukkan ɗarĩƙun sũfãye dõmin sunã rarraba mutãne ƙungiya-ƙungiya, kuma kõwa nã ganin abin da yake yi ko kuma wanda yake bi yã fi na wani. Kumawanda ke cikin wata ƙungiya bã zai iya haɗuwa da wata ba a lõkacin wurudinsu, a bãyan abũbuwan da suke ƙunsãwa a cikin ayyukansu na bidi'õ'i da aƙĩdõdi da suka sãɓa wa Musulunci.