Kur'an-ı Kerim meal tercümesi - Hausa Dilinde Tercüme - Ebubekir Cumi

Alishiqaq

external-link copy
1 : 84

إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنشَقَّتۡ

Idan sama ta kẽce, info
التفاسير:

external-link copy
2 : 84

وَأَذِنَتۡ لِرَبِّهَا وَحُقَّتۡ

Ta saurari Ubangijinta, kuma aka wajabta mata yin saurãron, info
التفاسير:

external-link copy
3 : 84

وَإِذَا ٱلۡأَرۡضُ مُدَّتۡ

Kuma idan ƙasã aka mĩƙe ta, info
التفاسير:

external-link copy
4 : 84

وَأَلۡقَتۡ مَا فِيهَا وَتَخَلَّتۡ

Kuma ta jẽfar da abin da yake a cikinta, tã wõfinta daga kõme. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 84

وَأَذِنَتۡ لِرَبِّهَا وَحُقَّتۡ

Kuma ta saurãri Ubangijinta, aka wajabta mata yin saurãren, info
التفاسير:

external-link copy
6 : 84

يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡإِنسَٰنُ إِنَّكَ كَادِحٌ إِلَىٰ رَبِّكَ كَدۡحٗا فَمُلَٰقِيهِ

Ya kai mutum! Lalle ne kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, To, kai mai haɗuwa da Shi ne. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 84

فَأَمَّا مَنۡ أُوتِيَ كِتَٰبَهُۥ بِيَمِينِهِۦ

To, amma wanda aka bai wa littãfinsa da damansa. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 84

فَسَوۡفَ يُحَاسَبُ حِسَابٗا يَسِيرٗا

To, za a yi masa hisãbi, hisãbi mai sauƙi. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 84

وَيَنقَلِبُ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦ مَسۡرُورٗا

Kuma ya jũya zuwa ga iyãlinsa (a cikin Aljanna), yanã mai raha. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 84

وَأَمَّا مَنۡ أُوتِيَ كِتَٰبَهُۥ وَرَآءَ ظَهۡرِهِۦ

Kuma amma wanda aka bai wa littãfinsa, daga wajen bãyansa. info
التفاسير:

external-link copy
11 : 84

فَسَوۡفَ يَدۡعُواْ ثُبُورٗا

To, zã shi dinga kiran halaka! info
التفاسير:

external-link copy
12 : 84

وَيَصۡلَىٰ سَعِيرًا

Kuma ya shiga sa'ĩr. info
التفاسير:

external-link copy
13 : 84

إِنَّهُۥ كَانَ فِيٓ أَهۡلِهِۦ مَسۡرُورًا

Lale ne shi, yã kasance (a dũniya) cikin iyãlinsa yanã mai raha. info
التفاسير:

external-link copy
14 : 84

إِنَّهُۥ ظَنَّ أَن لَّن يَحُورَ

Lalle ne yã yi zaton bã zai kõmo ba. info
التفاسير:

external-link copy
15 : 84

بَلَىٰٓۚ إِنَّ رَبَّهُۥ كَانَ بِهِۦ بَصِيرٗا

Na'am! Lalle ne, Ubangijinsa Ya kasance Mai gani gare shi. info
التفاسير:

external-link copy
16 : 84

فَلَآ أُقۡسِمُ بِٱلشَّفَقِ

To, ba sai Nã rantse da shafaƙi ba. info
التفاسير:

external-link copy
17 : 84

وَٱلَّيۡلِ وَمَا وَسَقَ

Da dare, da abin da ya ƙunsa. info
التفاسير:

external-link copy
18 : 84

وَٱلۡقَمَرِ إِذَا ٱتَّسَقَ

Da watã idan (haskensa) ya cika. info
التفاسير:

external-link copy
19 : 84

لَتَرۡكَبُنَّ طَبَقًا عَن طَبَقٖ

Lalle ne kunã hawan wani hãli daga wani hãli. info
التفاسير:

external-link copy
20 : 84

فَمَا لَهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ

To, mẽ ya sãme su, ba su yin ĩmãni? info
التفاسير:

external-link copy
21 : 84

وَإِذَا قُرِئَ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقُرۡءَانُ لَا يَسۡجُدُونَۤ۩

Kuma idan an karanta Alkur'ãni a kansu, bã su yin tawãli'u? info
التفاسير:

external-link copy
22 : 84

بَلِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يُكَذِّبُونَ

Ba haka ba! waɗanda suka kãfirta, sai ƙaryatãwa suke yi. info
التفاسير:

external-link copy
23 : 84

وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا يُوعُونَ

Alhãli Allah Shĩ ne Mafi sani ga abin a suke tãrãwa. info
التفاسير:

external-link copy
24 : 84

فَبَشِّرۡهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٍ

Saboda haka, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi. info
التفاسير:

external-link copy
25 : 84

إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَهُمۡ أَجۡرٌ غَيۡرُ مَمۡنُونِۭ

Fãce waɗanda suka yi ĩmãni, suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bã ya yankẽwa. info
التفاسير: