* A zãmanin Jahiliyya ana ƙullin amana a tsakanin ƙabilu ko a tsakanin mutum da wani mutum. Wannan ƙullin amãnar yakan haɗa har da sudusin dukiyar wanda ya mutu daga cikinsu. Wasu Musulmi sun shiga Musulunci a bãyan sun ƙulla irin wannan amãnar sabõda haka Allah Ya yi umurni da cika wannan alkawarin, kuma Ya kashe al'adar, Ya musanya ta da hukunce-hukuncen Musulunci. Kuma ana fassara masu ƙullin rantsuwa da masu gudãnar da aikin rabon dũkiyar gãdo. Ana biyan su ijãrar wahalarsu daga kãwunan magãda kamar yadda ya kamata.