Kur'an-ı Kerim meal tercümesi - Hausa Dilinde Tercüme - Ebubekir Cumi

Almu'aminoun

external-link copy
1 : 23

قَدۡ أَفۡلَحَ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ

Lalle ne, Mũminai* sun sãmi babban rabõ. info

* Mũminai su ne waɗanda suke da siffõfin da aka jeranta a cikin ãyõyĩn da ke biye daga ta 2 zuwa ga ta 9.

التفاسير:

external-link copy
2 : 23

ٱلَّذِينَ هُمۡ فِي صَلَاتِهِمۡ خَٰشِعُونَ

Waɗanda suke a cikin sallarsu mãsu tawãli'u ne. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 23

وَٱلَّذِينَ هُمۡ عَنِ ٱللَّغۡوِ مُعۡرِضُونَ

Kuma waɗanda suke, sũdaga barin yasassar magana, mãsu kau da kai ne. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 23

وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِلزَّكَوٰةِ فَٰعِلُونَ

Kuma waɗanda suke ga zakka mãsu aikatãwa ne. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 23

وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِفُرُوجِهِمۡ حَٰفِظُونَ

Kuma waɗanda suke ga farjõjinsu mãsu tsarẽwa ne. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 23

إِلَّا عَلَىٰٓ أَزۡوَٰجِهِمۡ أَوۡ مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُمۡ فَإِنَّهُمۡ غَيۡرُ مَلُومِينَ

Fãce a kan mãtan aurensu, kõ kuwa abin da hannayen dãmansu suka mallaka to lalle sũ bã waɗanda ake zargi, ba, ne. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 23

فَمَنِ ٱبۡتَغَىٰ وَرَآءَ ذَٰلِكَ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡعَادُونَ

Sabõda haka wanda ya nẽmi abin da ke bãyan wancan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙẽtarẽwar haddi. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 23

وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِأَمَٰنَٰتِهِمۡ وَعَهۡدِهِمۡ رَٰعُونَ

Kuma waɗanda suke, sũga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 23

وَٱلَّذِينَ هُمۡ عَلَىٰ صَلَوَٰتِهِمۡ يُحَافِظُونَ

Kuma da waɗanda suke, sũ a kan sallõlinsu sunã tsarẽwa. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 23

أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡوَٰرِثُونَ

Waɗannan, sũ ne magãda. info
التفاسير:

external-link copy
11 : 23

ٱلَّذِينَ يَرِثُونَ ٱلۡفِرۡدَوۡسَ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Waɗanda suke gãdõn (Aljannar) Firdausi,* su a cikinta madawwama ne. info

* Asalin firdausi fadama mai ruwa da itãce da ni'ima. Aljannar firdausi ita ce mafi ɗaukakar Aljanna.

التفاسير:

external-link copy
12 : 23

وَلَقَدۡ خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ مِن سُلَٰلَةٖ مِّن طِينٖ

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta mutum daga wani tsantsa daga lãka. info
التفاسير:

external-link copy
13 : 23

ثُمَّ جَعَلۡنَٰهُ نُطۡفَةٗ فِي قَرَارٖ مَّكِينٖ

Sa'an nan kuma Muka sanya shi, ɗigon maniyyi a cikin matabbata natsattsiya. info
التفاسير:

external-link copy
14 : 23

ثُمَّ خَلَقۡنَا ٱلنُّطۡفَةَ عَلَقَةٗ فَخَلَقۡنَا ٱلۡعَلَقَةَ مُضۡغَةٗ فَخَلَقۡنَا ٱلۡمُضۡغَةَ عِظَٰمٗا فَكَسَوۡنَا ٱلۡعِظَٰمَ لَحۡمٗا ثُمَّ أَنشَأۡنَٰهُ خَلۡقًا ءَاخَرَۚ فَتَبَارَكَ ٱللَّهُ أَحۡسَنُ ٱلۡخَٰلِقِينَ

Sa'an nan kuma Muka halitta shi gudan jini, sa'an nan Muka halitta gudan jinin tsõka, sa'an nan Muka halitta tsõkar ta zama ƙasũsuwa, sa'an nan Muka tufãtar da ƙasũsuwan da wani nãma sa'an nan kuma Muka ƙãga shi wata halitta dabam. Sabõda haka albarkun Allah sun bayyana, Shi ne Mafi kyawun mãsu halittawa. info
التفاسير:

external-link copy
15 : 23

ثُمَّ إِنَّكُم بَعۡدَ ذَٰلِكَ لَمَيِّتُونَ

Sa'an nan kuma ku, bãyan wannan, lalle ne masu mutuwa ne. info
التفاسير:

external-link copy
16 : 23

ثُمَّ إِنَّكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ تُبۡعَثُونَ

Sa'an nan kuma lalle ne kũ a Rãnar alkiyãma, za a iãyar da ku, info
التفاسير:

external-link copy
17 : 23

وَلَقَدۡ خَلَقۡنَا فَوۡقَكُمۡ سَبۡعَ طَرَآئِقَ وَمَا كُنَّا عَنِ ٱلۡخَلۡقِ غَٰفِلِينَ

Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta, a samanku, hanyõyi bakwai, kuma ba Mu kasance, daga barin halittar, Mãsu shagala ba. info
التفاسير: