* Ragõwar lõkacin cikin ko ƙãruwarsa.
* Hasken rãnã mai kama da ruwa ga idon mai dũbi daga nesa.
* Bãbu wani majiɓinci baicin Allah, wanda zai iya tsĩrar da su daga azãbarsa.
* Hĩla, ita ce mãkirci, Allah Yanã azabta mãsu yin hĩla ga addininsa, da azãba mai tsanani, kuma Ya kãmã su da hĩlarsu ta hanyar da ba su sani ba.