* Yũsufu yã shiga cikin fitinar uwar ɗãkinsa, Zalĩha. Yã mai da al'amarinsa ga Ubangijinsa wanda ya fitar da shi daga rĩjiya zuwa gidan sarautar Masar kuma Ya bã shi hukunci, watau Annabci da ilmi da Ya saukar masa na ibãda da mu'amãla. Ya sanar da shi halal da haram kuma ya sanya masa tsaro daga zunubi.
* Idan namiji da mace sun haɗu, to, bã ya halatta ga namijin ya dõgara ga ilminsa na amanarsa, ya zauna tãre da fitinar Shaiɗan. Sabõda haka Yũsufu ya gudu, ta bĩ Shi da hãlin kãsãwar mutum ga hãlin so har bãkin kõfa. Suka haɗu da mijinta. Ta mayar da maganar rawãtsa (ƙarya) a kan Yũsufu. Shi kuma ya kãre kansa da maganar gaskiya. Sai shaida zã a nema.Tã himmantu da dũkarsa dõmin yã ƙi ya yi mata ɗã'a ga abin da take so daga gare shi alhãli yanã bãwanta, shĩ kuma yã himmantu da dũkarta dõmin ya tunkuɗe macũci. Alfãshar ita ce zina, cũtar kuwa ita ce dũka, dalĩlin Ubangijinsa shĩ ne bin sharĩ'ar Allah.
* Bãyar da shaida a kan al'ãda, mai bãyar da shaidar yanã gabãtar da ita da magana a kan Yusufu, dõmin a ganinsa tuhuma a kanta, tã fi karfi, kuma zumuntarsa da ita ba ta ɗauke shi ba ga karkatar da magana dõmin ya taimake ta.
* Mai gida ya yi hukunci da yabon girman hãlin Yũsufu da kuma neman ya kashe maganar a nan.
* Tsegumin mãtã a cikin gari da yadda mãtar Azĩz ta yi maganin tsegumin, ta hanyar yiwa mãtan liyafa. Mace bã ta kunyar mãtã 'yan'uwanta ga irin wannan fitina idan ta sãme ta, ita kaɗai, balle mãtã ga sũ duka sun kãmu a cikin tarkon da ya kãma ta. Sai ta gaya musu gaskiyar abin da ya auku a tsakãninta da Yũsufu, a bãyan ta rãma zargin da suka yi mata.