Kur'an-ı Kerim meal tercümesi - Hausa Dilinde Tercüme - Ebubekir Cumi

Sayfa numarası:close

external-link copy
82 : 11

فَلَمَّا جَآءَ أَمۡرُنَا جَعَلۡنَا عَٰلِيَهَا سَافِلَهَا وَأَمۡطَرۡنَا عَلَيۡهَا حِجَارَةٗ مِّن سِجِّيلٖ مَّنضُودٖ

Sa'an nan a lõkacin da umurninMu ya je, Muka sanya na samanta ya zama na ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu a kanta (ƙasar Lũɗu) daga taɓocũrarre. info
التفاسير:

external-link copy
83 : 11

مُّسَوَّمَةً عِندَ رَبِّكَۖ وَمَا هِيَ مِنَ ٱلظَّٰلِمِينَ بِبَعِيدٖ

Alamtacce a wurin Ubangijinka. Kuma ita (ƙasar Lũɗu) ba ta zama mai nĩsa ba daga Azzãlumai (kuraishãwa). info
التفاسير:

external-link copy
84 : 11

۞ وَإِلَىٰ مَدۡيَنَ أَخَاهُمۡ شُعَيۡبٗاۚ قَالَ يَٰقَوۡمِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥۖ وَلَا تَنقُصُواْ ٱلۡمِكۡيَالَ وَٱلۡمِيزَانَۖ إِنِّيٓ أَرَىٰكُم بِخَيۡرٖ وَإِنِّيٓ أَخَافُ عَلَيۡكُمۡ عَذَابَ يَوۡمٖ مُّحِيطٖ

Kuma zuwa ga Madyana (Mun aika) ɗan'uwansu* Shu'aibu. Ya ce: "Ya Mutãnena! Ku bauta wa Allah. Ba ku da wani abin bautãwa fãce shi kuma kada ku rage mũdu da sikẽli. Lalle nĩ, inã ganin ku da wadãta**. Kuma lalle inã ji muku tsõron azãbar yini mai kẽwayẽwa." info

* Lãrabãwa ne, sunã zaune a tsakãnin Hijaz da Shãm. ** Inã ganin ku a cikin wadãta; bã ku da bukãtar rage wa mutãne kãyansu. Sabõda haka ku yi adalci ga mutãne wajen ciniki ya fi muku alheri daga dũkiyar haram mai ƙãrewa kõme yawanta.

التفاسير:

external-link copy
85 : 11

وَيَٰقَوۡمِ أَوۡفُواْ ٱلۡمِكۡيَالَ وَٱلۡمِيزَانَ بِٱلۡقِسۡطِۖ وَلَا تَبۡخَسُواْ ٱلنَّاسَ أَشۡيَآءَهُمۡ وَلَا تَعۡثَوۡاْ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُفۡسِدِينَ

"Ya mutãnẽna! Ku cika mũdu da sikẽli da ãdalci, kuma kada ku naƙasta wa mutãne kãyansu, kuma kada ku yi ɓarnã a cikin ƙasa kunã mãsu fasãdi." info
التفاسير:

external-link copy
86 : 11

بَقِيَّتُ ٱللَّهِ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَۚ وَمَآ أَنَا۠ عَلَيۡكُم بِحَفِيظٖ

"Falalar Allah mai wanzuwa ita ce mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance muminai, kuma ni bã mai tsaro ne a kanku ba." info
التفاسير:

external-link copy
87 : 11

قَالُواْ يَٰشُعَيۡبُ أَصَلَوٰتُكَ تَأۡمُرُكَ أَن نَّتۡرُكَ مَا يَعۡبُدُ ءَابَآؤُنَآ أَوۡ أَن نَّفۡعَلَ فِيٓ أَمۡوَٰلِنَا مَا نَشَٰٓؤُاْۖ إِنَّكَ لَأَنتَ ٱلۡحَلِيمُ ٱلرَّشِيدُ

Suka ce: "Yã Shu'aibu! Shin sallarka ce take umurtar ka ga mu bar abin da ubanninmu suke bautãwa, kõ kuwa mu bar aikata abin da muke so a cikin dũkiyõyinmu? Lalle, haƙĩƙa kai ne mai haƙuri shiryayye!" info
التفاسير:

external-link copy
88 : 11

قَالَ يَٰقَوۡمِ أَرَءَيۡتُمۡ إِن كُنتُ عَلَىٰ بَيِّنَةٖ مِّن رَّبِّي وَرَزَقَنِي مِنۡهُ رِزۡقًا حَسَنٗاۚ وَمَآ أُرِيدُ أَنۡ أُخَالِفَكُمۡ إِلَىٰ مَآ أَنۡهَىٰكُمۡ عَنۡهُۚ إِنۡ أُرِيدُ إِلَّا ٱلۡإِصۡلَٰحَ مَا ٱسۡتَطَعۡتُۚ وَمَا تَوۡفِيقِيٓ إِلَّا بِٱللَّهِۚ عَلَيۡهِ تَوَكَّلۡتُ وَإِلَيۡهِ أُنِيبُ

Ya ce: "Ya mutãnena! Kun gani idan no kasance a kan hujja bayyananniya daga Ubangijina, kuma Ya azurta nĩ da arzikimai kyãwo daga gare Shi? Kuma bã ni nufin in sãɓa muku zuwa ga abin da nake hana ku daga gare shi. Bã ni nufin kõme fãce gyãrã, gwargwadon da na sãmi dãma. Kuma muwãfaƙãta ba ta zama ba fãce daga Allah. A gare shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi na wakkala." info
التفاسير: