* Yã kãwo ƙãrin bayãni game da wannan ƙissa a cikin ãyõyin da ke tafe daga nan yadda bin addinin Allah yake da sauƙi a cikin lõkaci gajere na dũniya kawai a cikin taƙaitaccen lõkaci, da kuma wuyar bautawa wani ga ɗaukar kãya mãsu nauyi a dũniya da Lãhira, a cikin dõgon lõkaci.
* Ana siffanta duwãtsu maɗaukaka da ayyukan dũniya waɗanda bã ibãdar Allah ba, watau al'adu da ibãdõjin da ba ibãdar Allah ba, dukansu kõme yawansu zã su lãlãce a rãnar da Mai kira, wãtau lsrãfĩl, zai bũsa ƙaho na kiran mutãne zuwa ga Tãshin Ƙiyãma, kira wanda bãbu makarkata daga gare shi, watau bã kamar kiran da Annabãwa suka yi ba, wanda waɗansu mutãne suka karkace daga gare shi a nan dũniya.
* Bãbu ceto ga kõwa sai wanda Allah Mai rahama Ya yi masa iznin da yin ceton, ga wanda aka yi iznin sabõda shi, kuma izni anã yin sa ne da maganar Allah, ba da wata ishãra ba.