* Mũsã ya zãɓi mutun sabã'in daga Banĩ Isrã'ĩla, dõmin su tafi wurin Mĩƙãti tãre, su ji maganar Ubangiji. A lõkacin da ya yi kusa, sai ya yi gaggãwa dõmin bege. Kõ kuwa a bãyan azumin kwãna arba'in ya tafi a wurin Mĩƙãtin, Allah Ya fãra yi masa magana game da mutãnensa dõmin ɗebe masa kewa. Sai ya karɓa da cewa, "Sunã nan a kan sãwũna." Wãtau sunã nan a kan abin da na ɗõra su a kansa na addini da aƙĩda ta tauhĩdi. Sai Allah Ya ce masa "A'aha! sun musanya addininka da bautar maraƙi.".
* Alõkacin da Banĩ Isrã'ĩla zãsu fita daga Masar sun yi aron mundãyen mutãnen Masar dõmin su nũna cewa biki suke yi, bã gudu zã su yi ba, dõmin kada a bĩ su da wuri waɗannan mundãyen ne sãmiri ya tãra a bãyan tafiyar Mũsã zuwa ga Mĩƙãtin Ubangijinsa ya ƙera musu maraƙi mai jiki irin na mutãne da sauti irin na shãnu dõmin yã yi masa magudãnar iska a cikin cikinsa idan iskar ta fito, sai a jĩ ta da sauti kamar sautin kũkan shãnu. Kuma shi maraƙin bã ya dã wani rai, bã ya mõtsi, sai dai ƙũgin kawai.