ශුද්ධවූ අල් කුර්ආන් අර්ථ කථනය - හවුසියානු පරිවර්තනය - අබු බකර් ජූමි

Al'mudathir

external-link copy
1 : 74

يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡمُدَّثِّرُ

Yã wanda ya lulluɓa da mayãfi. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 74

قُمۡ فَأَنذِرۡ

Ka tãshi dõmin ka yi gargaɗi info
التفاسير:

external-link copy
3 : 74

وَرَبَّكَ فَكَبِّرۡ

Kuma Ubangijinka, sai ka girmama Shi, info
التفاسير:

external-link copy
4 : 74

وَثِيَابَكَ فَطَهِّرۡ

Kuma tutãfinka, sai ka tsarkake su, info
التفاسير:

external-link copy
5 : 74

وَٱلرُّجۡزَ فَٱهۡجُرۡ

Kuma gumãka, sai ka ƙaurace musu. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 74

وَلَا تَمۡنُن تَسۡتَكۡثِرُ

Kada ka yi kyauta kana nẽman ƙãri info
التفاسير:

external-link copy
7 : 74

وَلِرَبِّكَ فَٱصۡبِرۡ

Kuma sabõda Ubangijinka? Sai ka yi haƙure info
التفاسير:

external-link copy
8 : 74

فَإِذَا نُقِرَ فِي ٱلنَّاقُورِ

To, idan aka yi bũsa a cikin ƙaho. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 74

فَذَٰلِكَ يَوۡمَئِذٖ يَوۡمٌ عَسِيرٌ

To, wannan, a rãnar nan, yini ne mai wuya info
التفاسير:

external-link copy
10 : 74

عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ غَيۡرُ يَسِيرٖ

A kan kãfirai, bã mai sauƙi ba ne. info
التفاسير:

external-link copy
11 : 74

ذَرۡنِي وَمَنۡ خَلَقۡتُ وَحِيدٗا

Ka bar Ni da wanda Na halitta, yana shi kaɗai, info
التفاسير:

external-link copy
12 : 74

وَجَعَلۡتُ لَهُۥ مَالٗا مَّمۡدُودٗا

Kuma Na sanya masa dũkiya shimfiɗaɗɗiya info
التفاسير:

external-link copy
13 : 74

وَبَنِينَ شُهُودٗا

Da ɗiyã halartattu, info
التفاسير:

external-link copy
14 : 74

وَمَهَّدتُّ لَهُۥ تَمۡهِيدٗا

Kuma Na shimfiɗa? masa kõme shimfiɗãwa. info
التفاسير:

external-link copy
15 : 74

ثُمَّ يَطۡمَعُ أَنۡ أَزِيدَ

Sa'an nan, yanã kwaɗayin in yi masa ƙãri! info
التفاسير:

external-link copy
16 : 74

كَلَّآۖ إِنَّهُۥ كَانَ لِأٓيَٰتِنَا عَنِيدٗا

Faufau! Lalle ne, shĩ yã kasance, ga ãyõyin Mu, mai tsaurin kai. info
التفاسير:

external-link copy
17 : 74

سَأُرۡهِقُهُۥ صَعُودًا

Zã Ni kallafa masa wahala mai hauhawa. info
التفاسير:

external-link copy
18 : 74

إِنَّهُۥ فَكَّرَ وَقَدَّرَ

Lalle ne, Shi, yã yi tunãni, kuma yã ƙaddara (abin da zai faɗã game da Alƙur'ãni) info
التفاسير:

external-link copy
19 : 74

فَقُتِلَ كَيۡفَ قَدَّرَ

Sabõda haka, aka la'ane shi, kamar yadda ya ƙaddara. info
التفاسير:

external-link copy
20 : 74

ثُمَّ قُتِلَ كَيۡفَ قَدَّرَ

Sa'an nan, aka la'ane shi kamar yadda ya ƙaddara. info
التفاسير:

external-link copy
21 : 74

ثُمَّ نَظَرَ

Sa'an nan, ya yi tunãni info
التفاسير:

external-link copy
22 : 74

ثُمَّ عَبَسَ وَبَسَرَ

Sa'an nan, ya gintse huska? kuma ya yi murtuk. info
التفاسير:

external-link copy
23 : 74

ثُمَّ أَدۡبَرَ وَٱسۡتَكۡبَرَ

Sa'an nan, ya jũya bãya, kuma ya bunƙãsa, info
التفاسير:

external-link copy
24 : 74

فَقَالَ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ يُؤۡثَرُ

Sai ya ce: "Wannan abu dai bã kõme ba ne fãce wani sihiri, wanda aka ruwaito." info
التفاسير:

external-link copy
25 : 74

إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا قَوۡلُ ٱلۡبَشَرِ

"Wannan maganar mutum dai ce." info
التفاسير:

external-link copy
26 : 74

سَأُصۡلِيهِ سَقَرَ

Zã Ni ƙõna shi da Saƙar. info
التفاسير:

external-link copy
27 : 74

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا سَقَرُ

Kuma mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽwa Saƙar! info
التفاسير:

external-link copy
28 : 74

لَا تُبۡقِي وَلَا تَذَرُ

Bã ta ragẽwa, kuma bã ta bari. info
التفاسير:

external-link copy
29 : 74

لَوَّاحَةٞ لِّلۡبَشَرِ

Mai nãcẽwa ga jiki ce (da (ƙũna). info
التفاسير:

external-link copy
30 : 74

عَلَيۡهَا تِسۡعَةَ عَشَرَ

A kanta akwai (matsara) gõma shã tara. info
التفاسير:

external-link copy
31 : 74

وَمَا جَعَلۡنَآ أَصۡحَٰبَ ٱلنَّارِ إِلَّا مَلَٰٓئِكَةٗۖ وَمَا جَعَلۡنَا عِدَّتَهُمۡ إِلَّا فِتۡنَةٗ لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ لِيَسۡتَيۡقِنَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ وَيَزۡدَادَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِيمَٰنٗا وَلَا يَرۡتَابَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَلِيَقُولَ ٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٞ وَٱلۡكَٰفِرُونَ مَاذَآ أَرَادَ ٱللَّهُ بِهَٰذَا مَثَلٗاۚ كَذَٰلِكَ يُضِلُّ ٱللَّهُ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِي مَن يَشَآءُۚ وَمَا يَعۡلَمُ جُنُودَ رَبِّكَ إِلَّا هُوَۚ وَمَا هِيَ إِلَّا ذِكۡرَىٰ لِلۡبَشَرِ

Kuma ba Mu sanya ma'abũta wutã (wãto matsaranta) ba, fãce malã'iku, kuma ba Mu sanya adadinsu (gõma sha tara) ba, fãce dõmin fitina ga waɗanda suka kãfirta domin waɗanda aka bai wa littãfi su sãmi yaƙĩni kuma waɗanda suka yi ĩmãni su ƙãra ĩmãni, kuma waɗanda aka bai wa littãfi da mũminai bã zã su yi shakka ba, kuma domin wa ɗanda a cikin zukatansu akwai wata cuta da kãfirai su ce: "Mẽ Allah Yake nufi da wannan, ya kasance misãli?" Haka dai Allah ke ɓatar da wanda Ya so, kuma Ya shiryar da wanda ya so. Kuma bãbu wanda ya san mayãƙan Ubangijinka fãce Shi, kuma ita (wutar) ba ta kasance ba fãce wata tunãtarwa ce ga mutum. info
التفاسير:

external-link copy
32 : 74

كَلَّا وَٱلۡقَمَرِ

A'aha! Ina rantsuwa da watã. info
التفاسير:

external-link copy
33 : 74

وَٱلَّيۡلِ إِذۡ أَدۡبَرَ

Da dare a lõkacin da ya jũyar da baya. info
التفاسير:

external-link copy
34 : 74

وَٱلصُّبۡحِ إِذَآ أَسۡفَرَ

Da sãfiya idan ta wãye. info
التفاسير:

external-link copy
35 : 74

إِنَّهَا لَإِحۡدَى ٱلۡكُبَرِ

Ita (wutar) ɗayan manyan masĩfũ? ce. info
التفاسير:

external-link copy
36 : 74

نَذِيرٗا لِّلۡبَشَرِ

Mai gargaɗĩ ce ga mutum. info
التفاسير:

external-link copy
37 : 74

لِمَن شَآءَ مِنكُمۡ أَن يَتَقَدَّمَ أَوۡ يَتَأَخَّرَ

Ga wanda ya so, daga cikinku, ya gabãta ko ya jinkirta. info
التفاسير:

external-link copy
38 : 74

كُلُّ نَفۡسِۭ بِمَا كَسَبَتۡ رَهِينَةٌ

Kõwane rai ga abin da ya aikata jingina ce. info
التفاسير:

external-link copy
39 : 74

إِلَّآ أَصۡحَٰبَ ٱلۡيَمِينِ

Fãce mutãnen dãma. info
التفاسير:

external-link copy
40 : 74

فِي جَنَّٰتٖ يَتَسَآءَلُونَ

A cikin Aljanna suna tambayar jũna. info
التفاسير:

external-link copy
41 : 74

عَنِ ٱلۡمُجۡرِمِينَ

Game da mãsu laifi. info
التفاسير:

external-link copy
42 : 74

مَا سَلَكَكُمۡ فِي سَقَرَ

(Su ce musu) "Me ya shigar da ku a cikin Saƙar?" info
التفاسير:

external-link copy
43 : 74

قَالُواْ لَمۡ نَكُ مِنَ ٱلۡمُصَلِّينَ

Suka ce: "Ba mu kasance munã a cikin mãsu salla ba." info
التفاسير:

external-link copy
44 : 74

وَلَمۡ نَكُ نُطۡعِمُ ٱلۡمِسۡكِينَ

"Kuma ba mu kasance muna ciyar da matalautã ba." info
التفاسير:

external-link copy
45 : 74

وَكُنَّا نَخُوضُ مَعَ ٱلۡخَآئِضِينَ

"Kuma mun kasance muna kũtsãwa tãre da mãsu kũtsãwa." info
التفاسير:

external-link copy
46 : 74

وَكُنَّا نُكَذِّبُ بِيَوۡمِ ٱلدِّينِ

"Mun kasance munã ƙaryata rãnar sãkamako." info
التفاسير:

external-link copy
47 : 74

حَتَّىٰٓ أَتَىٰنَا ٱلۡيَقِينُ

"Har gaskiya (wãto mutuwa) ta zo mana." info
التفاسير:

external-link copy
48 : 74

فَمَا تَنفَعُهُمۡ شَفَٰعَةُ ٱلشَّٰفِعِينَ

Sabõda haka cẽton mãsu cẽto bã zai amfãne su ba. info
التفاسير:

external-link copy
49 : 74

فَمَا لَهُمۡ عَنِ ٱلتَّذۡكِرَةِ مُعۡرِضِينَ

Haba! Me ya same su, suka zama mãsu bijirewa daga wa'azin gaskiya. info
التفاسير:

external-link copy
50 : 74

كَأَنَّهُمۡ حُمُرٞ مُّسۡتَنفِرَةٞ

Kamar dai sũ, jãkuna firgitattu ne. info
التفاسير:

external-link copy
51 : 74

فَرَّتۡ مِن قَسۡوَرَةِۭ

Sun gudu daga zãki. info
التفاسير:

external-link copy
52 : 74

بَلۡ يُرِيدُ كُلُّ ٱمۡرِيٕٖ مِّنۡهُمۡ أَن يُؤۡتَىٰ صُحُفٗا مُّنَشَّرَةٗ

A'aha! Kõwãne mutum daga cikinsu yanã son a zo masa da takardu (da sũnansa) ana wãtsãwa info
التفاسير:

external-link copy
53 : 74

كَلَّاۖ بَل لَّا يَخَافُونَ ٱلۡأٓخِرَةَ

A'aha! Kai dai, bã su jin tsõron Lãhira. info
التفاسير:

external-link copy
54 : 74

كَلَّآ إِنَّهُۥ تَذۡكِرَةٞ

A'aha! Lalle ne, shi (Alƙur'ãni) tunãtarwa ce. info
التفاسير:

external-link copy
55 : 74

فَمَن شَآءَ ذَكَرَهُۥ

Dõmin wanda ya so, ya tuna. info
التفاسير:

external-link copy
56 : 74

وَمَا يَذۡكُرُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُۚ هُوَ أَهۡلُ ٱلتَّقۡوَىٰ وَأَهۡلُ ٱلۡمَغۡفِرَةِ

Kuma bã zã su tuna ba fãce idan Allah Ya so, Shi ne Ya cancanta a bi Shi da taƙawa kuma Ya cancanta ga Ya yi gãfara. info
التفاسير: