ශුද්ධවූ අල් කුර්ආන් අර්ථ කථනය - හවුසියානු පරිවර්තනය - අබු බකර් ජූමි

පිටු අංක:close

external-link copy
13 : 67

وَأَسِرُّواْ قَوۡلَكُمۡ أَوِ ٱجۡهَرُواْ بِهِۦٓۖ إِنَّهُۥ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ

Kuma ku asirta maganarku ko ku bayyana ta, lalle shi, (Allah), Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza. info
التفاسير:

external-link copy
14 : 67

أَلَا يَعۡلَمُ مَنۡ خَلَقَ وَهُوَ ٱللَّطِيفُ ٱلۡخَبِيرُ

Ashe, wanda Ya yi halitta bã zai iya saninta ba, alhãli kuwa shi Mai tausasãwa ne, kuma Mai labartawa? info
التفاسير:

external-link copy
15 : 67

هُوَ ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ ذَلُولٗا فَٱمۡشُواْ فِي مَنَاكِبِهَا وَكُلُواْ مِن رِّزۡقِهِۦۖ وَإِلَيۡهِ ٱلنُّشُورُ

Shi, (Allah), Yã sanya muku ƙasa hõrarriya, sai ku tafi cikin sãsanninta, kuma ku ci daga arzikin Sa, kuma zuwa gare shi ne tãshin yake. info
التفاسير:

external-link copy
16 : 67

ءَأَمِنتُم مَّن فِي ٱلسَّمَآءِ أَن يَخۡسِفَ بِكُمُ ٱلۡأَرۡضَ فَإِذَا هِيَ تَمُورُ

Shin kõ kun amince cewa wanda ke cikin sama, bã zai iya shãfe ƙasa tãre da ku ba, sai ga ta tana mai girgiza? info
التفاسير:

external-link copy
17 : 67

أَمۡ أَمِنتُم مَّن فِي ٱلسَّمَآءِ أَن يُرۡسِلَ عَلَيۡكُمۡ حَاصِبٗاۖ فَسَتَعۡلَمُونَ كَيۡفَ نَذِيرِ

Kõ kun amincẽ cewa wanda ke cikin sama bã zai iya sako muku iskar gũguwa ba? To, zã ku san yadda (ãƙibar) gargaɗi Na take. info
التفاسير:

external-link copy
18 : 67

وَلَقَدۡ كَذَّبَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ فَكَيۡفَ كَانَ نَكِيرِ

Lalle, waɗanda ke gabansu sun ƙaryata (manzanni). To, yãya (ãƙibar) gargaɗi Na ta kasance? info
التفاسير:

external-link copy
19 : 67

أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ إِلَى ٱلطَّيۡرِ فَوۡقَهُمۡ صَٰٓفَّٰتٖ وَيَقۡبِضۡنَۚ مَا يُمۡسِكُهُنَّ إِلَّا ٱلرَّحۡمَٰنُۚ إِنَّهُۥ بِكُلِّ شَيۡءِۭ بَصِيرٌ

Bã zã su yi dũbi ba zuwa ga tsuntsãye a kansu, mãsu sanwã, kuma suna fiffikãwa, bãbu mai riƙe da su sai (Allah), Mairahama? Lalle shi Mai gani ne ga dukan kõme. info
التفاسير:

external-link copy
20 : 67

أَمَّنۡ هَٰذَا ٱلَّذِي هُوَ جُندٞ لَّكُمۡ يَنصُرُكُم مِّن دُونِ ٱلرَّحۡمَٰنِۚ إِنِ ٱلۡكَٰفِرُونَ إِلَّا فِي غُرُورٍ

Wãne ne wanda zai zame muku mayãƙin da zai taimake ku, wanda bã (Allah) ba, Mai rahama? Kãfirai ba su a cikin kõme fãce rũɗu. info
التفاسير:

external-link copy
21 : 67

أَمَّنۡ هَٰذَا ٱلَّذِي يَرۡزُقُكُمۡ إِنۡ أَمۡسَكَ رِزۡقَهُۥۚ بَل لَّجُّواْ فِي عُتُوّٖ وَنُفُورٍ

Wãne ne wanda zai ciyar da ku, idan (Allah) Ya riƙe arzikin Sa? A'aha, sun yi zurfi cikin girman kai da tãshin hankali. info
التفاسير:

external-link copy
22 : 67

أَفَمَن يَمۡشِي مُكِبًّا عَلَىٰ وَجۡهِهِۦٓ أَهۡدَىٰٓ أَمَّن يَمۡشِي سَوِيًّا عَلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Shin, wanda ke tafiya a kife a kan fuskarsa yã fi zama a kan shiryuwa, ko kuwa wanda ke tafiya miƙe a kan hanya madaidaiciya? info
التفاسير:

external-link copy
23 : 67

قُلۡ هُوَ ٱلَّذِيٓ أَنشَأَكُمۡ وَجَعَلَ لَكُمُ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡأَبۡصَٰرَ وَٱلۡأَفۡـِٔدَةَۚ قَلِيلٗا مَّا تَشۡكُرُونَ

Ka ce: "(Allah) Shine Wanda Ya ƙaga halittarku, Ya sanya muku ji da gani da tunãni, amman kaɗan ce ƙwarai godiyarku!" info
التفاسير:

external-link copy
24 : 67

قُلۡ هُوَ ٱلَّذِي ذَرَأَكُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَإِلَيۡهِ تُحۡشَرُونَ

Kuma kace "Shi ne Ya halitta ku daga ƙasã, kuma zuwa gare Shi ne ake tãshin ku." info
التفاسير:

external-link copy
25 : 67

وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا ٱلۡوَعۡدُ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Kuma sunã cewa, "Yaushe ne wannan alkawarin zai tabbata in dai kun kasance mãsu gaskiya ne kũ?" info
التفاسير:

external-link copy
26 : 67

قُلۡ إِنَّمَا ٱلۡعِلۡمُ عِندَ ٱللَّهِ وَإِنَّمَآ أَنَا۠ نَذِيرٞ مُّبِينٞ

Ka ce: "Ilmin a wurin Allah kawai yake, kuma ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyana (gargaɗin)." info
التفاسير: