* Neman falala da sana'ar hannunsu, kõ fatauci, ba su zama nauyi a kan mutãne ba, kõwanensu ya dõgara ga Allah,sa'an nan yanã rãyuwa a kan hãlãliyarsa. ** Kufan sujuda, shĩ ne hasken fuskõkinsu da annurinsu. fuska ita ce madũbin zũciya. Anã gãne zũciyar ƙwarai daga fuskarta. Bã ya halatta ga mutum ya riƙa darkãka gõshinsa ga ƙasã dõmin ya yi kwãdon salla. Wannan alãmar riya ce. Faɗakarwa. Nan ne ƙarshen dõgãyen sũrõri da ake cewa Muɗawwalãtu. An ƙãresu da sũrõri biyu, Ƙitãl dõmin yãƙi, da fat'h dõmin tsãrin gudãnar da siyãsa sabõda tsaron Addĩni. Bãyan haka kuma sai gajerun sũrõri, watau Mufassalãtu.