* Hikima, ita ce Annabci, rarrabe magana, shĩ ne sanin hanyar yin sharĩ'a da rarrabe mai ƙãra daga wanda aka yi ƙãra, da neman shaidu daga mai ƙãra da neman rantsuwa ga mai musu.
* Dãwũda ya yi hukunci da zãlunci ga wanda ya yi ƙãra, sabõda abin da ya rufe shi na ƙin zãluntar mai rauni wanda Allah Ya hana. Nauyin wani laifi ya rufe shi daga tunãwa da wani laifi, watau yin hukunci tun binciken shari'a bai cika ba, sabõda iya maganar wani abõkin ƙãra. Wannan shĩ ne fitinar da ta same shi kawai kuma a kanta ya yi nadãma, kuma a kanta ne Allah Ya yi masa gargaɗin kada ya bi son rai mai sanya Fushi kõ yarda ga abin da bai cancanci haka ba. Yarda da wata ƙissar mãtar Uriya wadda Yahũdãwa ke sanyãwa, a nan, kãfirci ne ga Musulmi, dõmin ta kõre ismar Annabãwa, kuma ba ta dãce da lafazin Alƙur'ãni ba.