* Asalin mats'alar, tumãkin wani mutum suka yi kĩwon ɓarna a gõnar wani a cikin dare alhãli kuwa anã kallafa wa mai dabbõbi ya kange dabbõbinsa da dare kamar yadda ake kallafa wa mai shũka da tsare shũkarsa a cikin yini. Sai Dãwũdu ya yi hukunci da cewa mai shũkar ya mallaki tumakin, shi kuma mai tumãki ya mallaki shũkar ɓãtacciya. Sai Sulaimãn ya gyãra hukuncin da cħwa mai gõna ya riƙi tumãkin ya rãyu a kansu har a lõkacin da mai dabbõbin ya gyãra masa gonarsa har ta Koma yadda take a farKon lõkacin,sa'an nan ya mayar da tumãkin ya karɓi gõnarsa. A cikin ƙissar akwai nũnin cewa Annabãwa bã su saunar faɗin gaskiya, sabõda wani mutum duk yadda yake, kuma anã warware hukunci idan kuskure ya auku a ciki, kuma Annabãwa sunã yin kuskure ga abin da bai shãfi wahayiba. Kuma kõmãwa ga askiya idan tã bayyana wajibi ne.
* Wannan yanã nũna wajabcin yin sana'a wadda mutum ke rãyuwa a kanta. Kuma yanã nũna wajabcin aiki da sabubba dõmin neman tsaron kai. Bã ya halatta ga mutum ya yi kwance bãbu sanã'ar da zai tsayu a kanta Kõ kuma ya gĩtta kansa ga halaka da tãwilin tawakkali. Tawakkali shĩ ne mayar da ãƙibar al'amura ga Allah a bãyan mutum ya yi abinda yake iya yi.