* Watau dũtsen da ya gudu da tufafinsa ne a lõkacin da yake yin wanka dõmin a nũna wa Banĩ Isra'ila, waɗanda suka sõke shi da gwaiwa, cewa lãfiya lau yake. Kuma aka umurce shi da ɗaukar dũtsen, kuma yanzu aka umurce shi da ya dõke shi dõmin ruwa ya fito sabõda shansu.
* Alƙaryar ita ce Baitil Maƙdis, bisa shugabancin Yũsha'u. 'Saryarwa,' watau a saryar mana da zunubinmu, yã Allah!, 'Shiga ƙõfa da sujada,' watau da tawãli'u.
* Suka musanya hiɗɗa da hinɗa: watau alkama. (Aya ta 161) Sai aka saukar da azãba a kansu, sabõda haka wannan yã nũna cewa Allah ba ya son a musanya addininSa da kõme, sai dai mutum ya yi shi kamar yadda ya zo masa. Musanyawar umarnin, yãƙi ne a tsakãnin gaskiya da ƙarya. Ma'anar hiɗɗa ita ce kãyar da zunubi.
* Wata alƙarya anã ce da ita Ailata a bãkin gãɓar Bahr Al Kulzum a zãmanin Dãwũda, Allah ya umurce su a kan harshen Dãwũda su riƙi Jumma'a rãnar ĩdi, su yanke aiki a ciki, dõmin ibãda, sai suka ƙi Jumma'a suka zãɓi Asabar, ma'anarsa yankewa. To, sai Allah ya tsananta musu, Ya hana su farautar kĩfi a rãnar Asabar, Ya halatta musu shi, a sauran kwãnukan mãko. Sai a rãnar Asabar, su sãmi kĩfi wani kan wani, amma sauran kwanuka bã su sãmunsa haka. Sai Iblis ya sanar da su ga su aikata matarar ruwa a gefen tekun, a rãnar Asabar, su bũde kifi ya shiga su rufe, har rãnar Lahadi su kãma. Sai garin ya kasu uku: kashi ɗaya suka yi farauta, wasu suka hana, sũ kuma suka yi gãru a tsakãninsu da mãsu yi, na uku ba su yi farautar ba kuma ba su hana ba. A bãyan 'yan kwãnaki sai aka mayar da mãsu farautar birai, sa'an nan suka mutu.