Ibisobanuro bya qoran ntagatifu - Ibisobanuro bya Qur'an Ntagatifu mu rurimi rw'igihawusa - Abu Bakr Jomy.

numero y'urupapuro:close

external-link copy
59 : 40

إِنَّ ٱلسَّاعَةَ لَأٓتِيَةٞ لَّا رَيۡبَ فِيهَا وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يُؤۡمِنُونَ

Lalle Sa'a, haƙĩƙa mai zuwa ce, bãbu shakka a gare ta, kuma amma mafi yawan mutãne bã su yin ĩmãni. info
التفاسير:

external-link copy
60 : 40

وَقَالَ رَبُّكُمُ ٱدۡعُونِيٓ أَسۡتَجِبۡ لَكُمۡۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَسۡتَكۡبِرُونَ عَنۡ عِبَادَتِي سَيَدۡخُلُونَ جَهَنَّمَ دَاخِرِينَ

Kuma Ubangijinku ya ce: "Ku kira Ni in karɓa muku. Lalle waɗannan da ke kangara daga barin bauta Mini, za su shiga Jahannama sunã ƙasƙantattu." info
التفاسير:

external-link copy
61 : 40

ٱللَّهُ ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلَّيۡلَ لِتَسۡكُنُواْ فِيهِ وَٱلنَّهَارَ مُبۡصِرًاۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَشۡكُرُونَ

Allah ne Wanda Ya sanya muku dare dõmin ku natsu a cikinsa, da rãna mai gãnarwa. Lalle Allah, haƙĩƙa, Ma'abũcin falala ne a kan mutãne, kuma amma mafi yawan mutãne bã su gõdẽwa. info
التفاسير:

external-link copy
62 : 40

ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمۡ خَٰلِقُ كُلِّ شَيۡءٖ لَّآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ فَأَنَّىٰ تُؤۡفَكُونَ

Wancan shine Allah Ubangijinku, Mahaliccin dukan kõme, bãbu abin bautãwa fãce Shi. To, yãya ake karkatar da ku? info
التفاسير:

external-link copy
63 : 40

كَذَٰلِكَ يُؤۡفَكُ ٱلَّذِينَ كَانُواْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ يَجۡحَدُونَ

Kamar haka ake karkatar da waɗanda suka kasance sunã jãyayya game da ãyõyin Allah. info
التفاسير:

external-link copy
64 : 40

ٱللَّهُ ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ قَرَارٗا وَٱلسَّمَآءَ بِنَآءٗ وَصَوَّرَكُمۡ فَأَحۡسَنَ صُوَرَكُمۡ وَرَزَقَكُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَٰتِۚ ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمۡۖ فَتَبَارَكَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Allah ne Ya sanya muku kasã tabbatacciya, da sama ginanniya, kuma Ya sũranta ku, sa'an nan Ya kyautata sũrõrinku,, kuma Ya azurta ku daga abũbuwa mãsu dãɗi. Wancan Shĩne Allah Ubangijinku. To, albarkar Allah Ubangijin halittu tã bayyana. info
التفاسير:

external-link copy
65 : 40

هُوَ ٱلۡحَيُّ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ فَٱدۡعُوهُ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَۗ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Shĩ ne Mai rai, bãbu abin bautãwa fãce Shi. Sabõda haka ku kira Shi, kunã mãsu tsarkake addini a gare Shi. Gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu. info
التفاسير:

external-link copy
66 : 40

۞ قُلۡ إِنِّي نُهِيتُ أَنۡ أَعۡبُدَ ٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ لَمَّا جَآءَنِيَ ٱلۡبَيِّنَٰتُ مِن رَّبِّي وَأُمِرۡتُ أَنۡ أُسۡلِمَ لِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Ka ce: "Lalle nĩ, an hana ni in bauta wa waɗanda kuke kira waɗansun Allah a lõkacin da hujjõji bayyanannu suka zo mini daga Ubangijina, kuma an umurce ni in sallama ga Ubangijin halittu." info
التفاسير: